….GWAMNA DAUDA LAWAL YA MAIDA WA MINISTAN LABARAI MARTANI
Gwamna Dauda Lawal yau Talata, ya ce Gwamnatin Zamfara ta na da gamsassun hujjoji da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya da hannu a shirya zaman sulhu da ‘yan bindiga.
A jiya ne Ministan na Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ya zargi Gwamnatin Zamfara da siyasantar da lamarin tsaro. Biyo bayan neman ƙarin bayani da Gwamna Dauda ya yi kan zargin zaman sulhu ta ƙarƙashin ƙasa da ‘yan bindiga.
A wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Dauda Lawal tana da hujjoji masu tada hankali da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya kan sulhu da ‘yan bindiga.
Ya ƙara da cewa Ministan na Labarai ya yi ri-ga mallam masallaci wurin yanke hukunci tare da yankewa gwamnatin Zamfara hanzari.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mun nemi ƙarin bayani daga Gwamnatin Tarayya kan zaman sirri na sulhu da wasu jami’anta suke jagoranta a Jihar Zamfara ba tare da sanin Gwamnatin Jiha ko shugabanni jami’an tsaron jihar ba.
“Muna da gamsassun hujjoji da ke tabbatar da wannan zaman sulhu tsakanin jami’an Gwamnatin Tarayya da ‘yan bindiga a wurare mabambanta a Jihar Zamfara.
“Akwai ban takaici a ce Ministan Yaɗa Labarai zai fito bainar jama’a ya kore batun ba tare da ya nemi sani daga jami’an tsaro ko ‘yan uwanshi da ke da hannu dumu – dumu a lamarin ba. Mun tsammaci tun da ƙwararre ne a harka watsa labarai, zai bi matakan da ilimi ya sharɗanta don tabbatarwa kafin kore batun namu.
“Gwamnatin Jihar Zamfara tana matuƙar mutunta ƙa’ida tare da ganin ƙimar hukuma. Ba za mu fito kafafen watsa labarai muna fallasa sunayen jami’an Gwamnatin Tarayyan da ke wannan ta’asa ba, amma mun sanar da ‘yan Nijeriya don su nemi ƙarin bayani daga Gwamnatin ta Tarayya.
“Muna so mu sanar da Minista cewa jami’ansu na Gwamnatin Tarayya da ke jagorantar wannan zaman sulhu da ‘yan bindiga, sune ke siyasantar da matsalar tsaro, ba Gwamnatin Zamfara ba.
“Ba mu san daga inda Ministan ya samu ƙwarin gwiwar bugun ƙirji ya ce babu wani zaman sulhu da aka yi a Zamfara ba, saboda ai mun bayyana wuraren da aka yi waɗannan zama, irinsu Birnin Magaji, Maradun, Mun Haye, Ajah, Bawo, da kuma Bagega.
“Muna sake tunatawa cewa sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba. Sam! Ba wannan ba ne mafita ga matsalar, a yi amfani da qarfi kawai a kauda su, wanna ita ce matsayarmu har gobe.
“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina biye wa ‘yan amshin Shata, ta yi bincike tare da wanke kanta daga aikin waɗannan dillalan sulhu da ‘yan bindiga.”