Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da ɗorewar tsaftar muhalli da manufofin ƙarfafa al’umma su rungumi al’adar tsafta a Jihar Zamfara. A ranar Talata ne gwamnan ya ƙaddamar da rabon motoci da kayayyakin aiki daban-daban na shirin Tsaftar Muhalli na Matasan Zamfara a gidan …
Read More »ILIMI: GWAMNA LAWAL YA AMINCE DA ƊAUKAR MALAMAI 2,000 AIKI A ZAMFARA
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da ɗaukar malamai 2,000 aiki a faɗin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwar Jihar a ranar Litinin a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Gusau. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala …
Read More »SAMAR DA TSARO: GWAMNATIN ZAMFARA TA YABA WA SOJOJIN SAMA, TA KUMA JAJANTA WA AL’UMMAR DA HARIN JIRGIN SOJI YA SHAFA
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba da ƙoƙarin da sojojin Nijeriya ke yi na kai hare-hare kan ’yan bindiga ba ƙaƙƙautawa a jihar. A ƙarshen makon da ya gabata ne rundunar sojin saman Nijeriya ta kai wani samame kan ’yan bindigar da ke yunƙurin kai hari a ƙauyukan …
Read More »GWAMNA LAWAL YA GANA DA MINISTAN BUNƘASA KIWON DABBOBI, YA CE ZAMFARA TA SHIRYA WA KIWO
Daga Imrana Abdullahi Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwon Dabbobi cewa jihar Zamfara na da wuraren da za a yi kiwo. A ranar Alhamis ne gwamnan ya ziyarci hedikwatar ma’aikatar a wata ziyarar ban girma da ya kai wa ministan, Alhaji Idi Mukhtar Maiha. A …
Read More »GWAMNA DAUDA LAWAL YA AMINCE ƘARIN ALBASHIN WATA ƊAYA GA MA’AIKATAN ZAMFARA
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da biyan ƙarin albashin wata ɗaya ga ma’aikatan gwamnatin Jihar. Shugaban ma’aikata na jihar Zamfara ne ya sanar da hakan a wata takardar sanarwa da aka bayar a ranar 28 ga watan Disamba 2024. Albashin wata na 13 shi ne irinsa na …
Read More »GWAMNA LAWAL YA RATTABA HANNU KAN KASAFIN KUƊIN NAIRA BILIYAN 546 NA SHEKARAR 2025, YA SAKE ƊAUKAR ALƘAWARIN CETO JIHAR ZAMFARA
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira 546,014,575,000.00. Kasafin kuɗin 2025 mai taken; “Kasafin Ceto 2.0”, kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara ya gabatar wa gwamnan a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau. A yayin rattaba hannu kan …
Read More »GWAMNA LAWAL YA RABA KUƊAƊE SAMA DA NAIRA BILIYAN 4 NA SHIRIN NG-CARES GA MUTUM 44,000 A ZAMFARA
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon kuɗaɗe don tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a jihar. Rabon kuɗaɗen wani ɓangare ne na Farfaɗo da Ayyukan Tattalin Arziki da suka durƙushe a sanadiyyar COVID-19 na ‘NG-CARES’, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Garba Nadama, Sakatariyar JB Yakubu …
Read More »GWAMNA DAUDA LAWAL YA RANTSAR DA SABON KWAMISHINA, YA YI GARAMBAWUL A MUƘARRABANSA
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya yi garambawul a gwamnatinsa, sannan ya rantsar da wani sabon Kwamishina. A Litinin ɗin nan ne Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci zaman majalisar zartarwar jihar, inda a lokacin zaman ya rantsar da wani sabon Kwamishina. A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun …
Read More »GWAMNA LAWAL YA GABATAR DA KASAFIN KUƊIN NAIRA BILIYAN 545 NA SHEKARAR 2025 GA MAJALISAR ZAMFARA, YA BA DA FIFIKO KAN TSAR:O, LAFIYA DA ILIMI
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ɗaukar wani tsari mai inganci wajen tafiyar da harkokin kuɗaɗen jihar. A ranar Alhamis ne gwamnan ya miƙa wa Majalisar Dokokin Jihar Zamfara daftarin kimanin Naira Biliyan 545,014,575,000.00 a matsayin kasafin kuɗin shekarar 2025. A wata sanarwa da mai …
Read More »GWAMNAN LAWAL YA JADDADA ƘUDURINSA NA BAIWA ƁANGAREN SHARI’A ‘YANCIN KANSU DON SAMAR DA ADALCI A ZAMFARA
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta duƙufa wajen ba da fifiko ga tsare-tsare da ke inganta tabbatar da adalci a kan lokaci da kuma kare ’yancin ɓangaren shari’a. Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen taron ƙara wa …
Read More »