Wasu ‘yan kungiyar Oodua Nation (Yoruba Agitators) sun yi garkuwa da gidan rediyon Amuludun FM 99.1 da misalin karfe 6 na safiyar Lahadi a Ibadan.
Gidan rediyon na daya daga cikin na gwamnatin tarayya da kuma hukumar gidan rediyon tarayyar Najeriya FRCN.
Sai dai An kama biyar daga cikinsu da sanyin safiyar Lahadi.
Rahotanni sun ce maharan sun mamaye gidan rediyon da laya iri-iri inda suka mamaye gidan rediyon tare da watsa shirye-shirye kai tsaye.
Sun rike fastoci dauke da rubuce-rubucen, “Al’ummar Oodua ta zo ta zauna”, “Yoruba ba su karkashin tarayyar Najeriya”, majalisar dinkin duniya kwanan nan za ta ayyana kasar Oodua” da sauransu wadansu kalaman da suke rubuce kamar yadda suka yi su.
Babban Manajan gidan rediyon, Mista Stephen Agbaje, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
“Wasu gungun masu tayar da kayar baya sun zo da daddare, suka kwace tashar, amma jami’an tsaro sun shawo kan lamarin. Sun samu nasarar kwato tashar, kuma an kama wasu