Home / News / YAN SIYASA SU RIKA AMINCEWA DA KADDARA – MUSA HARO

YAN SIYASA SU RIKA AMINCEWA DA KADDARA – MUSA HARO

IMRANA ABDULLAHI
Alhaji Musa Haro Dan Madamin Daura Hakimin Dumurkul, ya jaddada kiran da yake yi wa al’umma a koda yaushe su rika amincewa da Kaddara a duk lokacin da aka yi zabe.
Alhaji Musa Haro, ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron hadin kai na mutanen masarautar Daura da kuma yayan jam’iyyar APC, ta yadda za a samu tafiya tare da Juna.
Ya ce hadin kai shi ne babban al’amarin da kowa ya dace ya Sanya a gaba, saboda sai da hadin kai sannan za a samu sukunin tafiya tare ayi taimakekeniya irin ta rayuwa.
Haro, ya ci gaba da cewa ya dace yan siyasa su Sani cewa tun ranar Gini ranar Zane ba wanda zai iya kawar da abin da Allah ya shirya zai faru.
“Ni kaina na ta ba yin takara a shekarun 2015 da 2019 amma wasu ne suka samu nasara wasu kuma sun fadi, amma duk mun je mun yi kira ga kowa sun kuma hakura sun biyo an ta fi tare.
“Kuma a tsarin siyasar Dimokuradiyya ba inda aka ce sai wane ko dan wane, ko a shekarar 2007 na yi takarar majalisar Jiha wani ne ya ci zaben na kuma yi masa tsakiya gida”.
Saboda haka nake yin kira ga duk wanda yake ganin bai samu nasara ba to, ya tsaya ayi da shi har a samu nasara, domin idan ma mutum ya ce zai je wata jam’iyya to da wane suna mutum zai je?
” Mu amince da Kaddara da ikon Allah mu kuma amince da shugabancin shugabannin mu, Malamai duk mu bisu”, inji Dan madamin Daura.
Sai ya ya ba tare da yi wa mai bayar da shawara ga jam’iyyar APC na kasa kan harkokin shari’a Ahmad Usman El – Marzuq, bisa kokarin da ya yi na kiran taron samun hadin kai a tsakanin yayan jam’iyyar APC, abin da ya bayyana da cewa hakan nasara ce babba kuma za ta haifar da samun da mai idanu.
“Mu so Juna ba hassada da Juna kuma duk wanda Allah ya ba mu kawai mu rungume shi a ta fi tare har a samu bukata ta biya nufi”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.