Home / Kasuwanci / ZA A BUDE KASUWAR DUNIYA TA KADUNA RANAR JUMA’A 3 GA WATAN FABRAIRU 2023

ZA A BUDE KASUWAR DUNIYA TA KADUNA RANAR JUMA’A 3 GA WATAN FABRAIRU 2023

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Mataimakin shugaban kasuwar duniya na 1 Mista Ishaya Idi, ya bayyana cewa a ranar 3 ga watan Fabrairu ne za a bude kasuwar duniyar kasa da kasa karo na 44 a matsugunnin kasuwar na dindindin da ke unguwar Rigachikun, Kaduna a tarayyar Najeriya.
Ishaya Idi ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da daukacin shugabannin kasuwar suka kira da aka yi a harabar kasuwar.
Ya bayyana cewa hakika kasuwar ta ba na al’amari ne mai matukar muhimmanci kwarai kasancewar lokaci ne da ya zo dai – dai da cikar kasuwar shekaru 50 da kafuwa kuma har yanzu ana cin kasuwar duk shekara ba a daina ba.
Ishaya Idi ya shaidawa manema labarai cewa kamar kowace shekara za a fara bude kasuwar ne da ake da ran shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai bude kasuwar a ranar Juma’a 3 ga watan Fairairu zuwa Lahadi 12 ha watan na Fabrairu 2023.
Hakika wannan kasuwar ta Bana na da matukar muhimmanci kwarai saboda ta zo dai- dai da lokacin da muke bikin murnar cika shekaru 50 da fara cin kasuwa don haka muke fatan zaku hada hannu tare da mu wajen bikin murnar Shakaru 50 da fara cin kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna.
Ana kuma saran muhimman mutane a ciki da wajen Najeriya tare da kamfanoni da yan kasuwa manya da kanana ne za su halarci kasuwar.
“Akwai muhimman tsare tsaren tsarin lafiyar jama’a da  dukiyarsu a lokacin cin wannan kasuwar.
Ishaya Idi shugaban baban kwamitin shirya kasuwar ta hannunsa na yi wa kowa fatan alkairi lokaci da bayan kammala wannan cin kasuwar duniyar kasa da kasa ta Kaduna.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.