Home / News / Za A Iya Samar Da Sabuwar Najeriya – Injiniya – Micheal Auta

Za A Iya Samar Da Sabuwar Najeriya – Injiniya – Micheal Auta

Imrana Abdullahi
An bayyana jam’iyyar Lebo a matsayin wadda za ta tabbatar da samar da sabuwar Najeriya domin ci gaban kasa tare da al’ummarta baki daya.
Injiniya Micheal Auta, wanda ke takarar neman zama dan majalisar Dattawa daga yankin Kudancin Kaduna, ya bayyana hakan a wajen wani gagarumin taron yayan jam’iyya da aka yi a Barnawa Kaduna da ya samu halartar yayan jam’iyyar daga daukacin yankin Arewa maso Yammacin kasar.
Micheal Auta, ya ci gaba da bayanin cewa sakamakon irin manufofin da jam’iyyar Lebo da ke da shi ne ya sa muke kokarin fadakar da al’umma su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jam’iyyar kwadago ta Lebo da ke nufin samar da ciyar da kasa gaba.
Auta, ya ci gaba da cewa “mutane su tambayi shin me wadanda suka rike manyan mukamai a Gwamnatin tarayya suka yi wa yankin Kudancin Kaduna, domin hakan zai taimakawa yankin da Jihar Kaduna baki daya”.
“Wadanda ke rike da makaman Gwamnati daga yankin Kudancin Kaduna sai dai kawai su rika bayar da wasu labarai ba gaira ba dalili, ba maganar aiki sai maganganu kawai”.
Micheal Auta, ya kara da cewa ” shin wadanda suka rike mukamin ministoci da sauran manyan mukamai daga Kudancin Kaduna shin me suka yi wa yankin, ya dace jama’a su tambaya”.
A misali Mista Auta wanda yake takarar neman zama dan majalisar Dattawa daga Kudancin Kaduna, ya tambayi kome wanda ya yi shugaban kamfanin matatar mai ta NNPC da ya samu a can baya wanda ya kasance daga yankin Kudancin Kaduna ne me ya aikatawa yankin, ba wani ko bangare na kamfanin NNPC da aka kawo Kudancin kaduna, Idan kuma akwai to, a fadi”.
Duk da cewa mun ba  su dama da yawa tun daga lokaci, kowace irin dama, amma babu wani abu da muka gani da za mu ce mun samu daga ribar damar da muka ba su, saboda haka mu rungumi jam’iyyar kwadago ta Lebo kawai domin kawo ci gaba mai ma’ana.
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar Lebo, Jonathan Asake cewa ya yi “duk mutanen dai da suka bata wa yan Najeriya su ne suka canza jam’iyya suna ci gaba da yin barnarsu da suka saba yi a can baya don haka jama’a su yi hattara da su”.
Ya kuma fadakar da mahalarta taron da aka yi a Kaduna cewa ya dace jama’a su Sani cewa duniya na kallon su kuma ba ruwan wani ko wasu da irin wadanda ke kokarin yin amfani da duk wani bambanci ko wani tunani sai dai kawai yin amfani da kwakwalwa da nufin samar da ci gaban kasa tare da al’ummarta gaba.
“Idan da akwai gaskiya da adalci tare da dai – daito zai taimakawa shugaba ya aiwatar da muhimman kudirorin da za su amfani al’umma baki daya”.
Saboda haka ne Jonathan Asake ya ce shi da kansa ya na son ya zamo a cikin jerin wadanda za su kawo canjin da zai amfani al’umma a kasa baki daya.
Daga cikin wadanda suka halarci taron na Kaduna akwai Sakatare Janar na jam’iyyar Lebo ta kasa Alhaji Umar Faruk Mai Rakumi, shigaban kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna kwamared Ayuba Magaji Suleiman, shugabannin jam’iyyar Lebo na Jihar Kaduna, Sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna Uwargida Christiana John Bawa da dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a jam’iyyar Lebo Mista Shinom Odinga, da ya yi jawabi mai ratsa zukata na kowa ya yi shirin yin aiki domin bayar da gudunmawarsa ba me za a samu ba. Da sauran yayan jam’iyyar da dama musamman masu yin takara a wasu matakai na Jiha, shiyya da sauransu.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.