Daga Imrana Abdullahi
Shugaban majalisar wakilai ta kasa Dokta Abbas Tajuddeen ya tabbatarwa yan Najeriya cewa sun je majalisar kasa ne a matsayin wakilan jama’ar da suka zabo su domin ba wai suna wakiltar kawunansu ba ne ko sun je majalisar domin biyan bukatun kansu kawai.
Dokta Abbas Tajuddeen ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wajen wani babban taron manema labarai na duniya da majalisar da yi a Abuja.
“Muna sane da irin halin rayuwar da jama’a ke ciki kuma muma muna jin irin yanayin da kowa ke ciki don haka muna kokarin kawo karshen matsalar da ikon Allah”.
Akwai wani babban taron da zamu kira domin a tattauna hanyoyin kara inganta al’amuran kasa, kuma za a yi wannan taron tattaunawa domin lalubo hanyoyin samar da ci gaban kasa tare da al’umma baki daya.
Rashin yi wa jama’a jama’ane ke haifar da matsalar jita- jita a duk abin da Gwannati ke kokarin yi, musamman a game da batun daukar wadansu bangarorin babban Bankin kasa na CBN zuwa Legas rashin yin bayanin dalilin hakan ne ya haifar da samun jita jita.
“Don haka ne nake yin kira ga dukkan bangarorin Gwamnatin kasa da su rika yi wa jama’a bayanin duk abin da za a yi ta yadda za a magance matsalar yan haifar da jita – jita”.
Abbas ya ci gaba da cewa wannan babban taron manema labarai na kasa shi ne na farko kuma hakan shi ne wani bangare na samar da canjin da ake bukata, ba tare da jin komai ba muna tabbatarwa da jama’ar kasa cewa babu wata tantama za a samu dukkan ci gaban kasa da kowa ke bukata.
“Muna yi wa yan Najeriya albishirin cewa majalisa ba za ta yi kasa a Gwiwa ba wajen samar da ci gaban da ake bukatar samu a Najeriya
Shugaban majalisar ya dai amsa dukkan tambayoyin manema labarai da suka yi masa a wajen wannan babban taron manema labarai na duniya da majalisar wakilan ta yi.