Daga Imrana Abdullahi
Sakataren jam’iyyar Lebo na kasa Umar Ibrahim Mairakumi, ya bayyana cewa Sakacin Gwannati ne ke kawo matsalar rashin tsaro sakamakon rashin adalci, yara sun kammala karatu ba abin yi har al’amura suka tabarbare a ko’ina.
Umar Ibrahim Mairakumi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Wannan lamarin da ke faruwa na tabarbarewar al’amura ci gaba ne daga abin da PDP ta bari a Najeriya baki daya.
“Mu a jam’iyyar Lebo tare da yan takararta baki daya zamu tabbatar da adalci da ci gaban kasa baki daya, saboda yan takarar mu a Jiha da kasa wato Peter Obi da Jonathan Asake duk suna da kyawawan shirye shiryen aiwatar da ayyukan ci gaban mata, matasa da tsofaffi da sauran yan kasa gaba a dukkan matakai a kasa.
“Jam’iyyun PDP da APC ne ake zargin sun kawo kabilanci a kasa domin dole ka zauna da kowa, idan Bayerabe ne, Inyamuri ko Bahaushe da duk ma kowane kabila ne na zai yuwu a canza sunayensu ba,haka abin yake, kuma dukkan kasuwancin arewacin Najeriya duk Inyamurai sun kwace kasuwancin, misali idan masu sana’ar Dabbobi ne, ko kayan Gona duk sai kaga Inyamuri a cikin kasuwar mu duk sun kace, komai kasuwar kauye sai kaga Inyamuri a can”
“Shugabanci da adalci ne ke haifar da ci gaban komai, idan kuwa aka ga sabanin hakan sai an ga ba dai dai ba”, Inji Mairakumi.
“Wasu na son dauwamar da mu cikin kunci da rashin adalci don haka jama’a kowa ya yi hattara wajen yin zabe, duk wanda ya zabi APC, to ya Sani ci gaban abin da PDP ta bari ne don haka jama’a su yi hattara”inji Umar Ibrahim Mai Rakumi.
Kuma muna yi wa kowa fatan alkairi da shigowa sabuwar shekara da fatan samun gagarumin ci gaba da karuwar arziki.