Home / News / MASU RUWA DA TSAKI A PDP NE SUKA CE A MAYAR WA DA YAN TAKARA KUDINSU – MAJIYA

MASU RUWA DA TSAKI A PDP NE SUKA CE A MAYAR WA DA YAN TAKARA KUDINSU – MAJIYA

IMRANA ABDULLAHI KADUNA
Sabanin irin yadda wasu kafofin yada labarai na Turanci da Hausa ke yadawa cewa wai dan tsohon mataimakin shugaban kasa da ya tsaya takarar neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar kujerar dan majalisar tarayya domin ya wakilci karamar hukumar Kaduna ta Arewa a majalisar dokoki ta kasa wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa masu ruwa da tsaki ne suka fitar da matsayar cewa duk wanda bai samu cin zaben ba ya je ya karbi kudinsa a hannun masu zaben (deliget) wanda zai tsaya wa jam’iyyar PDP takara.
Hakika labaran da wasu kafafen yada labarai ke yadawa cewa wai dan tsohon mataimakin shugaban kasa Adamu Muhammad Namadi Sambo ne ya cewa masu zaben dan takara a PDP su kawo masa kudinsa tun farko ba haka lamarin yake ba.
Majiyar mu ta ce ” masu ruwa da tsaki ne a jam’iyyar PDP wadanda su ne iyaye kuma Jagororin PDP baki daya suka ga irin yadda masu zaben dan takara da ake kira da (deliget) suka rika bin yan takara su na karbar makudan miliyoyin kudi daga hannun yan takarar neman a tsayar da su yan takarar majalisun dokoki na kasa da na Jihar ba dai – dai ba ne, kamar yadda samu cikakken bayani ma wani tsohon Gwamna ne ya fara kokawa da yadda lamarin ya kasance don haka ya fara cewa kowa ya karbi kudinsa in ba shi ne aka zaba ba, don haka irin yadda ake yadawa cewa wai dan tsohon mataimakin shugaban kasa ne ya ce a dawo masa da kudinsa tun da ba shi aka zaba ba lallai ba haka lamarin yake ba tun asali”.
Kamar dai yadda majiyar mu ta samu labari daga tushe cewa yan takarar majalisar dokokin Jihar Kaduna tuni sun karbi kudinsu daga masu zaben yan takara.
Sai kuma daga yan majalisar dokoki ta kasa wasu sun Karbe fiye da rabon kudinsu kuma a gobe za su kammala karbar nasu kudin baki daya.
Su dai yan takarar kujerar majalisar dokoki ta kasa a Jihar Kaduna musamman a karamar hukumar Kaduna ta Arewa sun ci karo da masu zaben yan takara ne wato (deliget) inda duk wanda ya karbi kudi daga wannan dan takara sai ya ta fi wajen wancan dan takara shima ya karbi na hannunsa kuma suna nuna wa dan takara ne naira miliyan uku aka ba su domin dan takarar ya san abin da yake ciki game da su in ya na son su bashi kuri’a.
“Wani dan takara ya ba deliget miliyan biyu da alkawarin in sun zabe shi zai cika masu miliyan daya sai kuma wanda ya ba su miliyan uku inda wanda aka zaba a karamar hukumar Kaduna ta Arewa ya ba su abin da ya fi duk wanda yan takara biyu suka bayar tare kuma da yi masu alkawarin cika masu kudi idan sun zabe shi.
” duk deliget daya dai ya na hada kudi naira miliyan Goma daga yan takara uku a karamar hukumar Kaduna ta Arewa wanda hakan abin duba wa ne in har ana son cimma muradin Dimokuradiyya.

“Mu a gobe idan Allah ya kai mu za mu kammala karbar kudin mu domin ya zuwa yanzu mun karbi kudi ya fi rabi daga hannun deliget”.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.