Home / KUNGIYOYI / Babu Yaki Tsakanin Al’ummar  Atyap Da Fulani A Kudancin Kaduna

Babu Yaki Tsakanin Al’ummar  Atyap Da Fulani A Kudancin Kaduna

Babu Yaki Tsakanin Al’ummar  Atyap Da Fulani A Kudancin Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
Kugabannin kungiyar al’ummar Atyap ta kasa karkashin jagorancin Samue Timbiwak Achie, sun bayyana wa duniya cewa ba suna cikin Yaki ba ne da mutanen al’ummar Fulani da ke yankin Kudancin Kaduna ko a ko’ina a fadin duniya.
Samuel Achie ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da suka kira a Kaduna.
Samuel, ya ci gaba da bayanin cewa su a iya saninsu wannan lamari Za’a iya bayyana shi a matsayin Shedanci ne ke kokarin faruwa tsakanin al’ummar Atyap da hausa Fulani domin a can baya lamarin na haka yake ba.
“Ni dinnan mina tare da Fulani tun ina yaro su na zuwa kiwon Shanu tare da Fulani idan za su ta fi Kiwo tare suke zuwa saboda tun da dadewa ana zaune wuri daya cikin kwanciyar hankali da lumana, to in ba Shedanci ba”, inji Samuel.
Samuel ya kara da cewa in ban da Shedanci ta yaya za a samu garuruwa a kalla 12 a yanzu duk an lalata su baki daya, an mayar da mutane sama da dubu biyar a yanzu duk su na sansanin yan gudun hijira kuma wadansu mutane a yanzu sun samu kansu a cikin wani mawuyacin hali.
“A masarautar Zagon Kataf ne zaka samu wakilin Hausawa, Fulani da kuma mazaba sukutum baki daya ta kasance ta al’ummar hausawa da Fulani ce suke zaben duk kansilan da suke so a koda yaushe domin ya wakilce su, idan kuma ana maganar Gonaki ko Filaye ne ai sai a bari Gwamnatin da ake cewa wuraren ta ne sai ta gudanar da aikin ta na rabawa jama’ar da ke cewa Gonakin su ne, amma irin wannan yanayin ba shi da wani amfani ko kadan”, in ji Samuel.
Sai dai ya fito fili ya shaidawa manema labarai cewa daga yanzu hakika ba za su kara bari irin hakan ta faru ba,”tun da dadewa a koda yaushe muna danne matasa kada su tashi domin yin ramuwar gayya a kan abin da aka yi masu, amma yanzu daga an kara yin hakan ba za a kara cewa kowa ya bari ba domin kowa a yanzu zai kare kansa ne kawai, saboda masu yi mana wannan Barnar sai sun kira sunayen mutane idan sun zo sannan su ce maka kwananka ya kare ka fito kawai”, inji Samuel Timbiwak Achie shugaban kungiyar al’ummar Atyap.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.