Home / News / AN YABAWA GWAMNA BELLO MATAWALLE NA ZAMFARA

AN YABAWA GWAMNA BELLO MATAWALLE NA ZAMFARA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

 

An yabawa Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Muhammad Bello Matawalle, bisa nadin da ya yi wa Dokta Suleiman Aliyu Shinkafi a matsayin mai ba Gwamna shawara a kan hulda da kasashen waje.

ALIYU MOYI DAN MADAMIN SHINKAFI, ne ya bayyana hakan a wajen wani babban taron da aka yi a garin Shinkafi.

Aliyu Moyi ya ci gaba da cewa hakika wannan kokari da Gwamnan Jihar Zamfara ya yi na nadin Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi abin farin ciki ne ga daukacin al’ummar karamar hukumar Shinkafi, da Jihar Zamfara baki daya.

Moyi ya kara da cewa daman can kamar yadda kowa ya sani Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi mutum ne da bashi da na biyu wajen kokari da jajircewarsa a koda yaushe ta fuskar Hidimtawa jama’a, don haka muke yin godiya kwarai da wannan nadin.

“Dama can su mai hannun roba ne kuma a halin yanzu duk kowa ya kama gabansa ba kowa sai wannan bawan Allah Inuwa baki kyamar kowa, Shalto kashe Kwarai da ke yi wa jama’a aiki a koda yaushe da nufin ciyar da al’umma baki daya gaba”.

Moyi dan madamin Shinkafi ya kuma yi kira ga Gwamna Muhammad Bello Matawalle, da ya daga darajar wannan kujera ta Dokta Suleiman Aliyu Shinkafi ya zuwa kwamishina domin kara samun inganta rayuwar mutanen Jihar Zamfara baki daya.

About andiya

Check Also

KATSINA IZALA GROUP CONSTRUCTS EYE HOSPITAL

  Work has been progressing steadily at the site for the construction of Eye Specialist …

Leave a Reply

Your email address will not be published.