Home / News / Arewa: Gwamna Tambuwal Baya Da Abokin Husuma Akan Neman Mulkin Najeriya

Arewa: Gwamna Tambuwal Baya Da Abokin Husuma Akan Neman Mulkin Najeriya

 

Gwamna jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal bai da wani abokin husuma ko jayayya ko hayaniya a duk yankin Arewa maso yamma saboda yana neman wata kujerar mulki a 2023.

Jita jita da wata kafar yada labarai mallakar wasu yan siyasa take yadawa, karya ne, neman suna ne, don kuwa babu wani abokin husuma ga Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal, bai kuma yarda da hakan ba ko a boye balle baiyane.

Masu neman yada wannan karya da cin fuska nayi ne don biyan wata bukata ta neman su kassara manyan dattawan arewa da manufar samun abin cefane.

Tun hawan karagar mulki na gwamnan jahar Sokoto, Gwamna Tambuwal yana aiki dare da rana, kafada kafada da dattawan arewa dake son ci gaba; ba kuma na yankin arewa maso yamma kadai ba, da dukkan yankin don nemo hanyoyin da zasu fadada da ciyar da yankin Arewa gaba, samun hadin kai da fahimtar juna a cikin girma da fahimta ga kowa.

Sakamakon haka yana da wuya mutum mai mutunci da daukaka, irin Gwamna Tambuwal ya shiga cikin yan gantalin neman kudin cefane don kassara wasu, yana da wahala ga mutum irinsa da ya samu nasara ta gina gida mai girma da daraja; har yazo daga baya yana neman ruguje shi saboda biyan wata bukata.

Muna kira ga sauran shugabani na Arewa su sani lokaci yayi da al’ummar Arewa zasu yiwa kansu karatun ta natsu ba don ra’ayin siyasa ba, sai don a samarwa yankin madogara mai amfani a cikin tafiyar zamani a yanzu.

Babu wanda yafi dan arewa kauna da son arewa, saboda haka dole ne yan arewa su hada kai da nemo hanyoyin ceto yankin da al’ummarsu muddin suna son a yarda dasu a girmmama su.

 

Daraja da daukaka ta Arewa itace tasu, muddin babu haka, tabbata Arewa na cikin yanayi na kaskanci da rashin tabbas da zai shafi sauran al’umma mai zuwa.

 

 

Yusuf Dingyadi, Sokoto
(SSA)
Hadimin Gwamna Tambuwal ne

About andiya

Check Also

An Yi Walimar Taya Soja Abdurrahman Abdullahi Shinkafi Murnar Zama 2nd Lieutenant A Kaduna

Daga Imrana Andullahi Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Mahmuda Aliyu Shinkafi, yi wa Allah godiya ya …

Leave a Reply

Your email address will not be published.