Home / Big News / Ba A Yi Zabe A Igabi Ba – Yan Takarar ADC

Ba A Yi Zabe A Igabi Ba – Yan Takarar ADC

 

Daga Imrana Abdullahi
Daukacin yan takarar da ke neman jam’iyyar ADC ta tsayar da su takarar kujerun Majalisar dokoki ta Jihar Kaduna daga mazabun Igabi ta Gabas da kuma Igabi ta Yamma duk sun tabbatarwa da manema labarai a Kaduna cewa Sam ba a yi zaben fitar da yan takara ba kamar yadda jam’iyyar ta shirya gudanarwa.
Yan takara a kalla mutum Tara da suka halarci cibiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna sun shaidawa manema labarai cewa a iya saninsu kuma a matsayinsu na yan takara duk sun tabbatar ba a yi zabe ba Sam a karamar hukumar Igabi domin a fitar da mutanen da za su tsaya wa ADC takarar majalisar Jiha domin karawa da sauran yan takara na jam’iyyu daban daban.
Kamar yadda Sagir Yusuf Liman da kuma Adamu Shu’aibu Gadar Gayan da dukkansu suka kasance yan takarar majalisar dokokin jihar Kaduna daga mazabun Igabi ta Gabas da ta Yamma duk sun tabbatar da cewa ba a yi zaben fitar da yan takara ba kamar yadda dokar jam’iyyar ta tanadar.
“Amma abin mamaki sai kawai muka wayi gari an fitar da sakamakon zaben da bai gudana ba Sam”.
Kamar yadda suka bayyana duk tare da xaukacin yan takarar sun ce suna son shaidawa jagororin jam’iyyar cewa sun ba su Awanni ashirin da hudu da su dauki matakin yin gyaran da ya dace ko kuma su yan takarar su dauki mataki a bisa doka domin nemo hakkinsu da na magoya bayansu da ke a Mazabu daban daban na fadin karamar hukumar ta Igabi.
Sun koka a kan cewa an karya dukkan ka’idojin gudanar da zaben fitar da yan takara na Hukumar Zabe da kuma na jam’iyyar ADC don haka ba ayi zaben fitar da Gwani na Sam, amma sun ce wa manema labarai sai kawai aka ɗauki damar aka bayyana sunan wadansu masu Uwa a Murhu da suka kasance yan shalele da suka bayyana da shafaffu da Mai, don haka ba su amince ba Sam da yin hakan.

About andiya

Check Also

New Dangote Transport Safety Policy Yielding Positive Result Says FRS FRSC Credits Dangote Transport For Improved Road Safety In Nigeria

      The Federal Road Safety Corps (FRSC) has commended Dangote Cement Transport for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.