Daga: Shuaibu Idris Miqati mni
Barka da yamma ga ‘yan jarida da daukacin al’umma.
Za ku tuna cewa watanni kadan da suka gabata, sakamakon rikice-rikicen da suka dabaibaye Jam’iyyar PDP, da dama daga cikinmu muka fice daga jam’iyyar. Wasu sun koma jam’iyyar APC mai mulki, yayin da wasu da dama suka shiga wasu jam’iyyu ciki har da ADC.
Ni na kasance daga cikin wadanda suka shiga jam’iyyar ADC bisa ka’ida da manufa, domin na yi imani cewa manyan ‘yan siyasa sun koyi darasi daga yadda ake tafiyar da jam’iyyu a Najeriya, kuma za mu yi kokarin kawo sauyi mai kyau da gaskiya.
Hakika, burina da addu’ata shi ne jam’iyyar ADC ta zama ingantacciyar madadin shugabanci – ta fuskar tsari, nagarta, da yadda ake gudanar da mulki. Mun fara gina jam’iyyar da sadaukarwa domin amfanin ‘yan Najeriya. Kuma kokarin ya haifar da ‘ya’ya, domin yanzu jam’iyyar ta zama karfi a bangaren adawa, tana kalubalantar gwamnati a kowane mataki.
Sai dai, daga yadda ma’aikatan sakatariyar jam’iyyar a hedikwatar kasa ke gudanar da ayyukansu, zuwa yadda aka tafiyar da tsarin zabin ‘yan takara, akwai abubuwa da dama da suka ba mu mamaki. Shugaban jam’iyya na kasa, Cif Dr. Sen. David B. Mark, ya taba bayyana cewa za a yi la’akari da kwarewa, gogewa, ilimi, da hikima wajen zabar a kalla kashi 60% na ‘yan takara bisa cancanta.
Mun shiga jerin taruka da ganawa da ‘yan jam’iyya, shugabanni, masu ruwa da tsaki, da ‘yan takara tare da kwamitin zabe. Mun bayyana damuwarmu kan rashin tsari mai kyau, amma duk da haka muka ci gaba da amincewa, har muka rattaba hannu kan yarjejeniya (MoU) da kwamitin zabe.
Abin takaici, tsarin zaben ya kasance cike da matsaloli, musamman rashin isasshen kudi, rashin ma’aikata, da kuma karancin kayan aiki da ya kamata domin gudanar da zabe mai gaskiya da adalci. Saboda wadannan matsaloli, kwamitin zabe ya tilasta yin gyare-gyare da ka iya lalata ingancin tsarin.
Abin da ya kara tayar mana da hankali shi ne yadda aka bai wa ma’aikatan ‘yan takara damar gudanar da zaben, ba tare da horaswa ko cikakken bayani ba. Wannan ya bude kofar magudi, zamba, da rashin gaskiya. Babu yadda za a samu sahihin sakamako a irin wannan tsari.
Daga abin da muka gani, tsarin zaben tun farko an shirya shi ne ya gaza, kuma hakika ya gaza kwarai. An kwace kayan zabe, an karkatar da tsarin, kuma muna da hujjoji da aka rubuta a bidiyo da ke nuna magudi. An yi amfani da ‘yan daba, makamai, da kuma bada cin hanci a fili.
Dangane da haka, ina kira ga mambobin kwamitin zabe da su tsaya kan gaskiya da mutunci, su soke wannan zabe baki daya. Mutunci da darajar ku na da muhimmanci, kuma ya kamata ku kare su.
Ni ba zan amince da sakamakon wannan zabe ba, saboda dukkan matsalolin da aka ambata. Ina kira ga kwamitin zabe da su kasance masu adalci, su yi aikinsu da gaskiya da rikon amana. Allah Madaukakin Sarki zai saka muku da alheri idan kuka yi haka.
Haka kuma, akwai wurare da dama a jihar da ba a gudanar da zabe kwata-kwata ba.
Muna sa ran ganin matakan da za ku dauka cikin gaggawa.
Shuaibu Idris Miqati mni
Dan takarar gwamna, Jam’iyyar ADC, Jihar Kaduna
THESHIELD Garkuwa