Home / News / Ba Za Mu Bayar Da Ranar Zabe Ba – Wusono

Ba Za Mu Bayar Da Ranar Zabe Ba – Wusono

Mustapha Imrana Abdullahi
Sakataren jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna Alhaji Ibrahim Aliyu Wusono ya bayyana cewa su a matsayinsu na yayan PDP a Jihar Kaduna ba za su bayar da wata ranar yin zaben kananan hukumomi kamar yadda hukumar zabe ta SIECOM ta bukace su su yi ba.
Ibrahim Aliyu Wusono ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan hukumar zaben Jihar Kaduna ta KAD- SIECOM ta sanar cewa ta dage lokacin gudanar da zaben da ta shirya yi.
Ibrahim Aliyu Wusono ya ce su a matsayinsu na jam’iyyar PDP ba za su bayar da wata ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi ba, “amma dai mun shirya yin zabe ko yau ko gobe za a yi shi duk a shirye muke ba wata tantama”.
Ya shaidawa manema labarai cewa hukumar zaben ta dai dage zaben ne domin kawai ta ba APC ne kawai ta gyara kurakuran da ta yi na kasa gudanar da zabe a kananan hukumomi sama da Goma, wanda mun aikawa da hukumar zabe wannan a rubuce domin tunatar da hukumar halin da ake ciki”.
“Muna kara tabbatarwa da hukumar zabe da kowa cewa mun rigaya mun shirya tsaf za mu yi zabe domin mun tsayar da dukkan Kansiloli da shugabannin kananan hukumomi a kananan hukumomi 23 a Juhar Kaduna”, inji Wusono.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.