Home / News / BAN FITA APC BA – SANATA KABIRU MARAFA

BAN FITA APC BA – SANATA KABIRU MARAFA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
TSOHON SANATA Kabiru Garba Marafa daga Jihar Zamfara ya bayyana cewa har yanzu ba su fice daga cikin jam’iyyar APC ba.
Tsohon Sanatan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta Tambarin hausa.
Kabiru Garba Marafa ya bayyana cewa a iya saninsa akwai jam’iyyu da yawa da suka nemi tattaunawa da su sakamakon irin yadda tsofaffin shugabannin APC na kasa suka yi masu kuma har yanzu su na tattaunawa da su.
Amma batun ficewa daga APC shi bai san wannan ba kuma kowa ya bayar da sanarwar hakan kuskure ya yi domin kamar yadda suke tattaunawa da sauran wasu jam’iyyu haka PDP ma ta nemi su tattauna kuma har yau ba a kammala tattaunawar ba.
Don haka ba gaskiya ba ne ni ko mu mun koma PDP sam ba a yi wannan ba, ana dai tattaunawa da jam’iyyu kuma sun ce za su yi mana abin da aka kasa yi mana a APC.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.