Home / MUKALA / BURIN MU SARKIN SHANU DA MATAWALLE KAWAI

BURIN MU SARKIN SHANU DA MATAWALLE KAWAI

Kowama ya faɗi, idan dai matawalle ya koma,Kowama ya faɗi idan  Sarkin Shanu ya zama shugaban karamar hukumar Shinkafi.
Al’ummar Jahar Zamafar da kuma al’ummar ƙaramar hukumar mulkin shinkafi za su yi mamaki cewar da nayi kowa ya faɗi idan dai matawalle da sarkin Shanu suka ci zaɓe,dalilina a nan shi ne fashion fahimce ni da kyau ku gane me nake nufi.
A duk faɗin ƙaramar hukumar mulkin shinkafi da Jahar Zamfara babu mai iya Sadaukar da ransa da dukiyarsa domin ceto Al’umma kamar wadannan mutane gida biyu bayun, a duk faɗin Jihar Zamafara da kuma girman ƙaramar hukumar mulkin shinkafi babu mai iya mulkin da mai ita mulkin da mai girma Gwamnan jihar Zamfara ya yi.
Ku lura  al’umma da wani abu guda ɗaya shin kun san Gwamna Bello Matawallen Maradun bai kwana ashirin a Office ba sai da ya ɗauki matasa Gurbin neman ilimin boko suka yi tattaki har  zuwa ƙasashen waje sama da mutum 1000 ya Bi yawa  makaranta tun daga farko har ƙarshensu shekara huɗu.
Abu Na farko da Gwamna Bello muhammad Matawallen Maradun ya yi wadda ya ba kowa sha’awa shi ne  duk Illahirin al’ummar da ke zaune Jahar Zamfara ya yi farin cikin haka a lokacin.
Shin kusan Gwamna Bello Muhammad matawalle Maradun ya taimaki matasa bayan da ya kai kwana Ɗari a kan kujerar Gwamnan Jihar Zamfara
Gwamna ya samarwa matasa aikin “n- power” duk watan Allah wanda ya samu zai ƙarɓi Naira dubu Talatin (30,000) ba ƙakkautawa.
Shin kasan Gwamna Bello Muhammad matawallen Maradun yana da shekara ɗaya ya fara ɗaukar ma ‘aikata Gwamnati Misali malamman karantarwa, malamman lafiya, da kuma bayar da wasu mukamai a matakin Gwamnati sosai da sosai.
Shin kun san Gwamna Bello Muhammad matawalle Maradun yana da shekara 2 ya bada damar a fara gina filin jirgin sama wanda duk tsawon Shekarun da muka yi bamu samu ikon yin Wannan aikin filin saukar Jirgin Sama ba.
Shin kasan Gwamna Bello muhammad matawallen Maradun Barden Kasar Hausa Shatiman Daular Usmaniyya khadimul ƙur’an yana da shekara 3 ya fara nada mutane sosai wanda Kafin sa ba a taba samun wata Gwamnatin da ta yi hakan ba
A kan wadannan dalilan nake son idan sai Gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun ya koma, to, duk wanda zai faɗi ya faɗi a zaben shekarar 2023.
Wani zai ce sarkin Shanu fa to saurara kaji wanene DOKTA SULAIMAN SHU’AIBU SHINKAFI SARKIN SHANUN SHINKAFI na farko, Kuma wane dalili ne yasa nake cewa idan buƙatar shi ta biya kowa ya rasa.
Dokta sulaiman Shu’aibu Shinkafi sarkin Shanun Shinkafi wallahi talahi billahi ita ce rantsuwar musulmi kuma ita ce koda gaskiya ba’a yinta,  amma akwai dalilin da ke sa ayi ta don wasu na cewa idan ka ji mutum na rantsuwa to ba shi da gaskiya wani ko koda zai rantsuwa zaka fahinci da gaskiyarshi yake rantsuwar a bisa dai dai.
Mu a karamar hukumar Shinkafi da ke cikin Jihar Zamfara kusan mun fi kowa samun muƙammai a wannan Gwamnatin da Dokta Bello muhammad matawallen Maradun ke yi wa jagoranci, wallahi, tun daga SSA, SA, DG. Kwamishina da dai sauran abubuwan alkairi da yawa da Gwamna Matawalle ke samarwa a wannan Gwamnatin.
Kuma muna da Ci gaba da shi kansa Gwamna idan zai fara taimako da shinkafi yake farawa kuma har gobe mai girma Gwamna Shinkafi a idon sa take na ya ga ya yi ƙoƙarin ƙara kawo Dauwamammen zaman lafiya tare da bada tattalin arziki ga ƙaramar hukumar mulkin shinkafi.
Amma abin da ke ciwa talakawan Shinkafi tiwo a ƙwarya shi ne duk wadanda aka nada a wani mukami cikin wannan Gwamnatin kamar irinsu “SSA, DG da kuma kantoman ƙaramar hukumar mulkin da sauran masu muƙammai babu wanda ya taɓa taimakawa gurin kawoma mai girma Gwamna ci gaba, a bisa taimakon da ya yi masu koko suka taimakawa Jam’iyar APC don samun Nasara komawar Gwamna Bello muhammad matawallen Maradun, Barden kasar Hausa.
Inbanda Dr sulaiman Shu’aibu Shinkafi, sai shugaban jam’iyya Alhaji Ibrahim Bama Shinkafi.
Wallahi ni shaida, ne kan haka a kan idanuna nake gani iya ƙoƙarin da sarkin Shanun Shinkafi ke yi na ganin faɗakar da al’ummar Shinkafi yake ta fama yi a kullum.
Don haka ne bisa wannan dalilin  Naga  yakamata mai girma Gwamna Muddin kana son Kaga ci gaban al’ummar ƙaramar hukumar mulkin shinkafi kana son Kaga so ci gaban Jam’iyar APC to, a taimakamana ka bamu Dokta Sulaiman Shu’aibu Shinkafi sarkin Shanun Shinkafi na farko a matsayin shugaban ƙaramar hukumar mulkin Shinkafi.
 Abubakar Lauwali kaura Shinkafi Ne ya rubuto wannan 

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.