Home / News / Dubban Magoya Bayan Jam’iyyar APC A Jihar Zamfara Sun Fito Zaben Shugabannin Mazabu

Dubban Magoya Bayan Jam’iyyar APC A Jihar Zamfara Sun Fito Zaben Shugabannin Mazabu

…. Ya’yan Jam’iyyar sun tabbatar da Gwamna Matawalle a matsayin Jagora
Daga Imrana Abdullahi
Dubban magoya bayan jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara  suka fito domin zaben sababbin shugabanninsu a matakin mazabu guda dari da Arba’in da Bakwai wanda aka gudanar a ranar  Assabar.
Yan jaridun da suka zagaya wuraren gudanar da zaben sun lura da cewa an gudanar da taron cikin kwanciyar hankali a daukacin mazabu 147, duk da kalubalen tsaro da ake fuskanta a jihar.
Mata da matasa masu yawa ne suka halarci taron yayin da kwamitin gudanar da taron suka hallara domin sanya ido kan yadda lamarin yake gudana cikin lumana.
A unguwannin Galadima da Kayyaye/Matusgi da ke karkashin kananan hukumomin Talatar Mafara, an gudanar da taron jam’iyyar APC lami lafiya, ba tare da wani tashin hankali ba.
Haka ma a wasu Mazabu na kananan Hukumomin Mulkin Maradun, Tsafe, Kauran Namoda da Gumi an ga magoya bayan jam’iyyar APC sun fito tun da sanyin safiya suna jiran masu lura da zaben.
Kafar yada labarai ya Kamfanin dillancin labarai ya kasa tare da jarida “The Sun” duk sun lura da yadda al’amura ke gudana a kananan hukumomin  biyu na Talata Mafara da Gusau inda rahotanni suka bayyana cewa  ‘ya’yan jam’iyyar sun fito da yawansu domin halartar zaben.
Honarabul Musa Bawa Musa Yankuzo, Shugaban kwamitin zabe a karamar hukumar Tsafe.
Irin wannan rahotanni a sauran sassan jihar na cewa mambobin zartaswar jam’iyyar sun fito ne ta hanyar fahimtar juna.
Sani Maigadi daga unguwar Galadinma da ke karamar hukumar Talata Mafara, wanda wakilinmu ya zanta da shi ya yaba wa Gwamna Bello Matawalle bisa tabbatar da an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci..
“Wannan tsarin gwamnatin ya na daya daga cikin tsari mafi kyawu a jihar don haka muna godiya ga mai girma gwamna bisa tabbatar da hadin kan jam’iyyar APC. Babu wani takunkumi kuma an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.” Inji shi.
Shugabar mata ta unguwar Galadinma, Hajiya Husseina Talatar Mafara ta ce APC ta zama babbar jam’iyya tun bayan hawan Gwamna Bello a matsayin uban jam’iyyar a jihar.
Shugaban karamar hukumar Talata Mafara, Honorabul Dahiru Maiyara, ya yabawa ‘ya’yan jam’iyyar bisa gudanar da taron unguwanni kyauta a fadin karamar hukumar.
Dahiru ya hori sabbin zababbun shugabannin jam’iyyar da su kasance masu gaskiya da riko da ‘ya’yan jam’iyyar wajen tafiyar da al’amuran jam’iyyar.
An gudanar da taron ne a karkashin kulawar Alhaji Ibrahim Kabir Masari, wanda ya jagoranci kwamitin babban taron jam’iyyar APC na kasa a jihar.
Da yake jawabi ga ‘ya’yan jam’iyyar kafin a fara taron, Masari ya ce, “hedikwatar jam’iyyar ta kasa ta amince da gudanar da taron a jihar Zamfara.
Wannan shi ne karo na farko da aka fara gudanar da taron jam’iyyar APC a jahar Zamfara cikin kwanciya hankali tun bayan komawar Gwamna Bello Muhammad Belli Matawalle cikin  jam’iyyar APC daga PDP.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.