Home / News / GIRGIZAR KASA TA KAMA PDP A ZAMFARA DAN TAKARAR MAJALISA YA KOMA APC

GIRGIZAR KASA TA KAMA PDP A ZAMFARA DAN TAKARAR MAJALISA YA KOMA APC

Daga Imrana Abdullahi
Kwanaki biyar bayan dan takarar majalisar dokokin Jihar Zamfara a mazabar Gusau II, Alhaji Ibrahim Mada ya yaga satifiket dinsa na shaidar cin zabe domin tsayawa takara wanda aka bashi karkashin PDP bayan ya canza sheka zuwa APC, sai ga kuma wani da zai tsaya takara daga mazabar Talatar Mafara ta Arewa ya canza shima inda ya bi guguwar share PDP domin ya koma jam’iyyar APC a Jihar Zamfara.
Dan takarar PDP daga Mafara ta Arewa domin zuwa majalisar Jihar, Honarabul Umar Yahaya ya koma APC ya kuma bar takararsa.
Ya kuma samu kyakkyawar tarba daga shugabannin APC a Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Honarabul Dokta Bello Muhammad Matawalle tare da shugaban APC na Jiha Honarabul Tukur Umar Dan Fulani a cikin gidan Gwamna a garin Gusau.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Yusuf Idris Gusau, sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a Jihar Zamfara.
Umar Yahaya ya ce hukuncin da ya dauka na yin watsi da takararsa karkashin PDP ya koma APC duk saboda rikicin da jam’iyyar PDP ne ke fama da shi a dukkan mataki tun daga na kasa zuwa Jiha.
Ya kuma kara da cewa shugabancin PDP ya cika kama karya wanda sam ba a sauraren wani abu daga yayan jam’iyyar.
Ya bayyana tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Dauda Lawal Dare wanda babban kotun Gwamnatin tarayya ta kora, a matsayin wani mutum mai kayan siyasa da ke zaune a Abuja kuma bai shirya sauraren kowa ba balantana ya koya daga tsofaffin hannu.
Umar Yahaya ya ci gaba da cewa, ba a iya ganin Dauda ba a iya samunsa koda manyan shugaban jam’iyyar na Jiha duk kuwa kowa ne irin yanayi aka shiga.
Ya kuma yi bayanin cewa dukkan mambobin PDP duk sun fara fahimtar irin yadda lamarin yake musamman ma cewa Dauda ba mutum ba ne da za a iya dogaro da shi a siyasance da kuma sauran mu’amalar rayuwa, saboda haka da yawa daga cikin mambobin PDP kwannan nan za su shigo cikin jam’iyyar PDP.
Da yake yin maraba da shi zuwa babbar jam’iyyar ceton kasa tare da al’ummarta baki daya, Gwamna Bello Matawalle cewa ya yi jam’iyyar APC da ke tafiya da dukkan mambobinta baki daya, saboda haka Gwamnan ya tabbatar masa da cewa bashi da wani bambanci ko kadan da sauran mambobin da ya iske a cikinta.
Gwamnan ya kuma ya ba da irin kokarinsa da matakin da ya dauka da ya komo bangaren masu son ci gaba tare da aiwatar da aiki a Jihar Zamfara, sai ya shawarce shi da ya kara fadakar da sauran mambobin PDP su koma APC domin hada hannu a ciyar da Jihar Zamfara gaba.
Gwamna Matawalle ya kara da cewa Gwamnatin da yake yi wa jagoranci ta yi kokari kwarai a game da harkokin tsaro, samar da ababen more rayuwa, samar da ayyukanyi da kuma tabbatarwa an yi tafiya da kowa a harkar tafiyar da Gwamnati.
Taron dai ya samu halartar Sanata Kaboru Garba Marafa da Honarabul Abubakar S/ Pawa Dambo da dai sauransu.

About andiya

Check Also

Our Mandate Is To Organise Congresses, Says Labour Party Transition Committee Chairman, Umar

  Former president of the Nigerian Labour Congress, NLC, and Transition Committee chairman of the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.