Home / News / Har Yanzu Shehu Sani Na Jam’iyyar PRP

Har Yanzu Shehu Sani Na Jam’iyyar PRP

Har Yanzu Shehu Sani Na Jam’iyyar PRP
 Imrana Abdullahi
Sanata Shehu Sani da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawan Nijeriya tsawon shekaru hudu ya bayyana cewa har yanzu ya na nan a cikin jam’iyyar ceton Talakawa mai suna PRP.
Shehu Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambaya a kafar Talbijin ta Arise, a wani shirin da ake yi wa masu tattaunawa a cikinsa tambayoyi a game da batun zabe, tsaro da kuma batun sake fasalin Nijeriya.
“Ni ina nan cikin jam’iyyar PRP wadda ita ce mai alkibla da kuma kishin talakawan kasa baki daya, wadda take kokarin wayar da kan jama’a su san yankinsu kuma nan gaba kadan za mu kaddamar da batun siyasa”.
Ya ci gaba da cewa kwanan nan ne ma muka rasa shugaba baki daya Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa  da Allah ya yi wa Rasuwa.
Da yake amsa tambaya a kan ko masu satar jama’a na cikin birane, sai Shehu Sani ya ce hakika zai iya amincewa da hakan domin kuwa zai yi wahala idan ka ce dukkan wuraren da masu kashe kudi domin abubuwan alfarma suke zuwa kaga wadancan irin mutane masu karbar kudin fansa da ake cewa suna cikin daji, don haka komai zai iya kasancewa su na dajin ana amfani da su ne a tura su gaba kawai,wasu na Karbe zaren.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.