Home / News / Kada Kowa Ya Kai Kara Kotu – Mamadi

Kada Kowa Ya Kai Kara Kotu – Mamadi

Mustapha Imrana Abdullahi
Honarabul Muhammad Abubakar Mamadi ya yi kira ga daukacin yayan jam’iyyar APC da ke karamar hukumar Igabi su dari uku da Talatin 332 da suka tsaya takara da kada su je kotu, domin sun dauki matakin yi wa kowa adalci.
Honarabul Muhammad Abubakar Mamadi ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron yayan jam’iyyar da aka yi a ofishinsa da ke Rigachikun karamar hukumar Igabi.
Abubakar Mamadi ya ce ” muna yin kira ga duk wanda ya sa yi fom na tsayawa takara da kowa ya yi hakuri saboda tuni an mika komai ga Allah kuma ana ganin hasken lamarin, don haka ba batun zuwa kotu domin an bi hanyar da ta dace kuma za a cimma nasara”, inji Mamadi.
Ya kara da fadakar da yayan jam’iyyar cewa babu inda aka ta ba cewa gaskiyar mutum ta kare sai dai karya ta kare kawai.
Mamadi ya kuma fadakar da yayan jam’iyyar da cewa “shin wadanda kuka ga an rubuta da biro kun ga an Rantsar su na murna? Ai kowa ya san babu wani abu mai kama da hakan don haka kada aje kotu nasara na nan zuwa idan Allah ya yarda”, inji Mamadi.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Barista Ibrahim Bello Rigachikun wanda ya kasance tsohon dan majalisar tarayya ne ya yi kira ga yayan jam’iyyar masu ingantattun takardun da suka biya kudin Fom domin tsayawa takara da su yi hakuri domin nasara na nan tafe
Bello Rigachikun ya ci gaba da cewa akwai abin da ake cewa “haramtacce da kuma wanda yake na halak don haka mutane sama da dari uku da suke a wannan bangaren su ne halattattu kuma nan gaba kadan gaskiya za ta yi halinta”, inji shi.
Wasu daga cikin yayan jam’iyyar da suka halarci taron sun tofa albarkacin bakinsu na nuna goyon baya tare da yin jinjina ga Honarabul Muhammad Abubakar Mamadi da Barista Ibrahim Bello Rigachikun bisa irin kokarin da suke yi wajen kwato yancin jama’a.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.