Daga Imrana Abdullahi
Daukacin yayan kungiyar matasan Najeriya sun bayyana cikakken hadin kansu da goyon baya ga zababben Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari Shetiman Zamfara domin ya Dare kujerar shugaban majalisar Dattawa ta kasa.
Yayan kungiyar sun bayyana hakan ne a lokacin da suka kai wata ziyara ofishin hedikwatar jam’iyyar APC da ke babban birnin tarayya Abuja.
Matasan sun ce duk da irin matsayar da jam’iyyar APC ta nuna game da wanda take bukatar ya zama shugaba hakika duk da hakan su a matsayinsu na manyan Gobe da aka yi Gwagwarmayar siyasa da su har aka samu nasarar lashe zaben to a iya na su hangen Sanata Abdul’Aziz Yari Abubakar ne ya dace ya zama shugaban majalisa Dattawan Najeriya saboda hakan zai da ce kwarai wajen biyan muradun kasar.
Matasan sun kuma yi kira da babbar murya ga zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da ya duba irin yadda ake tafiya tare da yankin arewacin Najeriya da kuma yankin Kudu maso Yamma da yan al’ummar Yarbawa suka fi yawa, don haka ko domin hakan ya dace zababben shugaban kasar ya goyi bayan Sanata Abdul’Aziz Yari ya zama shugaban majalisar Dattawa ta Goma (10)
” Sanata Abdul’Aziz Yari mutum ne haziki mai kokari ga kwazon aiki domin ya na da masaniyar makamar aikin a koda yaushe, ya zama shugaban kungiyar Gwamnoni ta Najeriya kuma an ga irin yadda abubuwa suka ta fi Gwanin kyau a wajen tafiyar da kasa baki daya don haka mutum ne da ya dace ya zama shugaban majalisar Dattawa babu wata tantama ko kadan”, inji matasan.
Sun kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a tarayyar Najeriya da su tabbatar da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya wajen ganin Dimokuradiyya ta samu cin gashin kanta a koda yaushe domin hakan zai haifar da nasara kwarai.