Home / KUNGIYOYI / Kungiyoyin Biyar Sun Bukaci Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da El – Rufa’I A Matsayin Minista

Kungiyoyin Biyar Sun Bukaci Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da El – Rufa’I A Matsayin Minista

Daga Imrana Abdullahi

Gamayyar kungiyoyi biyar masu zaman kansu da ba ruwansu da siyasa da ke wadansu abubuwa masu kama da Juna da suka hada da zamantakewa, tattalin arziki da al’adu a karkashin jagorancin kungiyar ci gaban Tudun Wada Zariya mai suna “Tudun Wada Zaria Sustainable Development Association” sun bayyanawa  manema labarai a Kaduna, cewa suna yin kira da yawun al’umma da yawan mutanen da abin ya shafa da su wanke tare da tabbatar da Malam Nasir el-Rufai a matsayin ministan Gwamnatin tarayyar Najeriya.

Kungiyar ta yi zargin cewa akwai makarkashiyar hana tsohon Gwamnan Kaduna zama minista a wannan gwamnati mai ci, abin bakin ciki da suka yi nuni da cewa zai hana al’ummar kasa cin gajiyar kwarewa da gogewa da kuma gagarumar gudumawa daga tsohon Ministan babban birnin tarayya Abuja.

Membobin ƙungiyar sun ƙunshi;  Kungiyar Ma’aikatan Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya, Kungiyar Ci gaban Kasuwar Zamani ta Tudun Wada, Kungiyar Masu Babura da Direbobi, Zariya Progressive Animal Sellers and Rearing Multipurpose Cooperative Society and Waje Districts Development Association, Zariya, sun yi taro a Sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) Kaduna.

 Inda suka yi ta yabon elRufai a cikin shirin manema labarai da sakataren hadin gwiwa na kungiyar Alhaji Nasiru Ladan ya karanta.

Ladan ya ce “bai ga dalilin da zai sa ba za a wanke el-Rufai tare da tabbatar da shi ba duk da an gudanar da tsauraran matakai na tantancewa da jami’an tsaro daban-daban da sauran su yayin da aka tabbatar da sauran wadanda aka nada da ke gaban hukumar EFCC”, kamar yadda Ladan ya shaidawa manema labarai a Kaduna.

“El-Rufai ya kasance gwamnan da ya fi kowa iya aiki a tarihin jihar Kaduna bisa kyawawan nasarorin da ya samu da kuma ci gaban ayyukan more rayuwa daban-daban a fadin jihar da a yanzu kowa zai iya ganinsu”, inji gamayyar kungiyoyin.

“Don haka muna kira ga shugabannin majalisar dattawa da su gaggauta wanke El-Rufai tare da tabbatar da zaman lafiya da adalci tare da ci gaba,” inji shi.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.