Home / KUNGIYOYI / Lokaci Ya Yi Da Za Mu Hadu Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya- Fasto Buru

Lokaci Ya Yi Da Za Mu Hadu Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya- Fasto Buru

Lokaci Ya Yi Da Za Mu Hadu Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya- Fasto Buru
 Imrana Abdullahi
Fasto Yohanna YD Biru, shugaban cibiyar kokarin samar da zaman lafiya da dai- daitawa tsakanin Juna ta kasa ya bayyana cewa lokaci ya yi da dukkan jama’a ba tare da nuna bambance bambance ba za  su hadu a guri daya wajen samar da zaman lafiya da dai daitawa tsakanin Juna,musamman al’ummar Arewa da Nijeriya baki daya.
“Ina neman gafarar dukkan al’ummar musulmi a madadin al’ummar Kirista domin hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da taimakon Juna a koda yaushe”.
Ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron lacca karo na Goma (10) domin samar da zaman lafiya da kungiyar yan jarida Musulmi suka shirya da aka yi a dakin taro na gidan tunawa da Sardauna da ke Kaduna.
Inda ya ce hakika a wannan watan ne ya dace kowane mutum su tabbatar da an samu fahimtar Juna tsakanin musulmi da Kirista ta yadda za a samu ciyar da kasa gaba.
“Ina kokarin bayanin cewa tsakanin mu ya dace a yafewa Juna, mu a madadin Kiristoci duk abin da ke tsakaninmu mun yafewa kowa don haka muna fatan suma al’ummar musulmi za su yafe mana da nufin a ci gaban kowa baki daya”.
Da yake gabatar da jawabi shugaban kungiyar yan jarida Musulmi ta kasa Kwamared Jafaru Mai Tama cewa ya yi an kafa wannan kungiya ne da nufin fadakarwa domin samar da zaman lafiya da dai daito a tsakanin juna a dukkan mataki na kasa baki daya.
Da yake gabatar da Kasida mai taken rawar da kafafen yada labarai yakamata su taka, Alhaji Garba Abdulkarim Kumo kira ya yi ga wannan kungiya ta yan jarida ta kasa da su kara himma wajen kirkiro shirye shiryen samar da zaman lafiya a kafafen yada labarai.
Ya kuma yi fadakarwa a game da irin yadda wasu kafofin yada labarai ke kara taimakawa wajen raba kawunan jama’a bayyane ba tare da bin ka’idojin aikin jarida ba.
Ya zama dole ga dukkan dan jarida da duk wata kafar yada labarai ta zama a tsakiya cikin al’amuran jama’a ba tare da nuna bangaranci ko karkata wani bari ba.
“Ba za a samu zaman lafiya da ci gaban da ake bukata ba in har kafofin yada labarai ba su yi aikin da ya dace ba, na yin gaskiya da adalci ga kowa a kowane lokaci.
Ba wani tsarin aikin jarida da ya bayar da wata damar ayi bambanci ko bangaranci game da dukkan al’amarin jama’a.
Kumo, ya kuma yi kira ga manema labarai da su rika yin aikinsu bisa tsari da tanaje tanajen aikin jarida .
Ya dace yan jarida su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kansu ta fuskar fadakarwa da ilmantar da al’umma baki daya ta yadda kasa za ta samu ci gaba.
Da yake ta’aliki a game da ka’idar da aka gabatar a wajen taron tsohon Dan jarida Alhaji Tajudeen Ajibade fadakarwa ya yi cewa ba yan jarida ba ne kawai suke da bukatar kudi ba, dukkan bil’ Adama na bukatar kudi

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.