Maganin Mahaukacin Biri, Karen Maguzawa…!
Duk Daya Bayan Daya, Yau An Fara Dawo Ma Maganar Da Gwamnan Jahar Zamfara Bello Mutawalle Yayi Akan Bamu Da Karfin Soja Ko Na Yan Sanda Da Zamu Iya Kawo Karshen Kalubalen Nan, Har Sai Al’umma Sun Hada Kai Tare Da Samar Da Adalci a Tsakaninsu.
Inda Ya Kalubalanci Hukumomin Tsaro Da Su Hada Kai Tare Baiyana Gaskiya Lamari Ga Gwamnoni Don Shawo Kan Matsalar Tsaro Dake Addabar Al’umma Tare Da Amfani Da Dabarun Sulhu Da Yafiya Inda Zai Iya Ceto Rayuka Da Dukiyoyin Su.
Haka Ma A Fito Ayi Sulhu Tare Da Samar Da Hanyoyin Bunkasa Rayuwar Jama’a Da Magance Rashin Adalci Ga Wasu Jinsin Al’umma Da Ake Yiwa Kudin Goro Wajen Ramuwar Gayya; Ba Tare Da Nuna Rarrabewa Na Jinsi Da Akeyi Ba.
Yanzu Ga Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Furta Hakan Dangane Da Hanyoyin Da Aka Bi Na Ceto Daliban Jami’ar Koyon Aikin Gona Ta Afaka, Kaduna Da Kuma Kai Karshen Kalubalen Dake Gabanmu.
Haka Ma Ga Bayanin Wasikar Tsohon SGF Pius Anyim Akan Sake Duba Hanyoyin Samar Da Hadin Kai Da Rage Rashin Adalci Da Ake Yiwa Wasu Jinsin Al’umma A Kasarnan.
Matsalar Tsaro Ba Ta PDP Ko APC Bace; Ba Kuma Karfin Bindiga Kawai Ne Hanyar Magance Ta Ba, Mu Tuna Alkur’ani Yace; Sulhu Alheri Ne.
Siyasa Dabam, Ceto Rayukan Al’umma Dabam.
Bai Dacewa Kayi Watsi Da Al’umma Don Son Kai, Sa’ilin Kace, Kana Da Kishin Su Ba.
Daukar Matakai Na Hana Kisan Jama’a Da Kone Dukiyoyinsu Ko Satar Dabboninsu, Yafi Muhimmanci Da Kai Ziyarar Jaje Ko Ta’azziya Garesu.
Gwamnatin Tarayya Da Na Jihohi Nada Kalubale Mai Yawa, Ko Dai A Magance Hakan, Ko Kuma Ayi Ta Zama A Cikin Fargaba Da Rashin Tabbas.
Dr Gummi Ya Hango Hakan, Yayi Bayani, An Tura Masa Yan Yara Suna Zaginsa Da Aibanta Shi.
Darasi Daga Daliban Afaka Ya Ishi Misali Tun Da Mun Manta Da Na Jangebe Da Kagara Da Na Kankara.
Allah Ya Kara Ma Shugabani Hikima Da Basira Ga Fito Da Hanyoyin Ceto Kasarnan, Amin.
– Yusuf Dingyadi ne ya rubuto wannan makalar daga Sakkwato.