Home / News / Muna Fatan A Samu Wanda Zai Dora A Inda Buhari Ya Tsaya – Ambarud Sani Wali

Muna Fatan A Samu Wanda Zai Dora A Inda Buhari Ya Tsaya – Ambarud Sani Wali

IMRANA ABDULLAHI
An bayyana shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin mai yin aiki tukuru domin kafa Najeriya kan ingantacciyar turbar sahihin ci gaba mai dorewa.
Ambarud Yahya Sani Wali ce ta bayyana hakan lokacin da take ganawa da manema labarai a Daura.
Ambarud Sani Wali, ta ce daman tun farko kokarin da shugaba Muhammadu Buhari yake kokarin yi shi ne kafa kyakkyawar turbar ci gaban Najeriya domin Dora komai a bisa turbar da ta dace, kuma a halin yanzu shugaba Buhari na kokari kan aiwatar da hakan.
“Saboda haka muke kara yin kira ga daukacin yan Najeriya da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga shugaba Muhammadu Buhari domin ya sauke nauyin da ke kansa na jagoranci a kasa baki daya, kasancewar abin da shugaban yake yi aiki ne ba na mutum daya ba kowa sai ya bayar da cikakken hadin kai da goyon baya da nufin Bukata ta biya nufi”.
Ambarud, ta kuma yi kira ga daukacin al’umma baki daya da su bayar da hadin kai da goyon baya ga wanda jam’iyyar APC ta tsayar takarar shugaban kasa domin ya ci gaba da aiwatar da ayyukan alkairin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake domin kasa tare da jama’arta su kai ga nasara”,.
Haka zalika Ambarud Sani Wali, ta ce abu ne mai matukar muhimmanci ga jama’a su Sani cewa ya na da alfanu kwarai su ci gaba da bayar da hadin kai ga yan takarar da APC ta tsayar a dukkan matakai daban daban saboda a samu nasarar gudanar da jagorancin al’ummar kasa.
Sai ta kara fadakar da jama’a game da muhimmancin kowa ya tabbatar da duk wanda ya Isa kada kuri’a da ya karbi rajistar da za ta bashi damar yin zabe a shekarar 2023 mai zuwa.
Ta kuma ce su masu aikin yin rajista da kuma yi wa jama’a katin dan kasa da su ci gaba da yin hakuri da jama’a saboda wasu da yawa ba su san muhimmancin yin katin ba, amma idan aka yi hakuri aka kuma fadakar da jama’a sai a yi wa kowa da ya Isa zabe ayi masa rajistar ko kuma ga yan kasa a yi masu katin dan kasa”.
“Akwai lokacin da muka yi aikin hadin Gwiwa tare da matar Gwamna aka rika biyan kudin Babura ga mutane su je ayi masu rajista domin sanin muhimmancin kuri’ar lokacin zabe da kuma bayan zaben”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.