Home / News / Saboda Abdul’Aziz Yari Nake APC – Dokta Shinkafi

Saboda Abdul’Aziz Yari Nake APC – Dokta Shinkafi

Mustapha Imrana Abdullahi
Wani jigon jam’iyyar APC daga Jihar Zamfara Dokta Suleiman Aliyu Shinkafi ya bayyana cewa shi ya na yin jam’iyyar APC ne saboda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Abubakar Yari, kasancewarsa jagora na kwarai.
Dokta Suleiman Aliyu Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Dokta Shinkafi ya ci gaba da cewa sakamakon irin duban da ya yi na nazari a game da nagartar tsohon Gwamnan sai ya ga cewa babu wani jagoran da ya wuce Abdul’Aziz a duk siyasar Jihar Zamfara domin shi ne ke rike da dukkan al’umma baki daya.
“Abdul’aziz ne fa mutumin da yake rike da mutanen Jihar Zamfara baki daya domin irin abubuwan alkairin da yake bazawa a Jihar Zamfara kowa na amfana da du har wadanda ba yayan jam’iyyar APC ba kuma duk ana godiya tare da su, ko a kwanan nan sai da ya sayo Takin zamani aka ba manoma a cikin rahusa domin su ci gaba da Noma a wadata kasa da abinci, ban da batun Azumi, Sallah babba da karama kai ko a yanzu Raguna na nan ya na ta taimakawa bayin Allah don su samu sukunin yin layya cikin sauki a wadata, kuma a lokacin Sallah karama zai taimakawa kowace mazaba da Shanu a yanka kowa ya kai Nama gidansa”. Inji Shinkafi.
Saboda haka a hakikanin gaskiya ni ina son gayawa duniya cewa ina siyasa ne musamman jam’iyyar APC saboda wannan jajirtaccen jagora Alhaji Abdul’Aziz Yari kuma duk umarnin da ya ba mu shi za mu bi, in zama a jam’iyyar APC ko akasin hakan duk ni da jama’ata a shirye muke”.

About andiya

Check Also

CCMMD Urges Unified Action to End Gender-Based Violence in Nigeria Amidst UN 16 Days of Activism with Hope and Action

As the world commence the celebration of International Day for the Elimination of Violence against …

Leave a Reply

Your email address will not be published.