Home / News / Tsarin Jam’iyya Ne Ke Hada Kan Al’ummar Najeriya – Gwamna Yobe

Tsarin Jam’iyya Ne Ke Hada Kan Al’ummar Najeriya – Gwamna Yobe

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kwamitin rikon jam’iyyar APC  na kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Bunu ya bayyana tsarin jam’iyya a matsayin abin da ke hada kan dimbin al’ummar Najeriya ba tare da nuna wani bambanci ba.
Gwamna Mai Mala Buni ya ce hakika babu wani abin da ke hada kan mutane su kasance wuri daya kamar tsarin jam’iyya da ake da shi a Najeriya.
“Za ka ga mutane daban daban suna gudanar da huddosinsu ba tare da nuna bambancin addini, kabila ko wani bangaranci ba kokarin kowa dai shi ne a samu nasara a duk lokacin da za a gudanar da wani aikin jam’iyya”.
Saboda haka batun Gwamnan Jihar Zamfara zai koma APC a ranar Talata sai a bari kawai sai ranar Talatar aga me zai faru?
“Amma dai batun da wasu ke yi na kada a kasa samun yan Adawa a Najeriya Mai Mala Buni ya bayar da shawarar cewa ya dace mutane su rika duba irin yadda kasar Cana take da suke da jam’iyya daya kuma ba su ci baya ba don haka tsarin jam’iyya na kawo hadin kai har ma ya ce babu wani tsarin da yake kawo hadin kan jama’a, ya dai yi wannan bayanin ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da kafar yada labarai ta bbc hausa”.
Gwamna Mai Mala Buni ya kuma yi bayanin cewa aikin samar da rajistar yayan jam’iyya, wanda a can baya jam’iyyar APC na da yawan mambobi miliyan 19 ne kawai amma sakamakon aikin da muka yi a halin yanzu na sabunta rajistar sunayen yayan jam’iyyar APC a duk fadin Najeriya baki daya a yanzu muna da yawan yayan jam’iyya da suka kai akalla miliyan Arba’in da doriya kuma aiki ne da aka bari a bude da kowa zai iya yin rajista a duk karamar hukumar da yake”, inji Mai Mala Buni.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.