Daga Imrana Abdullahi
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’Aziz Yari Abubakar, ya Karyata Jita jitar da wadansu ke yadawa cewa wai zai ce a zabe shi sannan kuma kada a zabi sauran yan takara, musamman Gwamna.
Abdul’Aziz Yari Abubakar, wanda dan takarar Sanata ne a halin yanzu a Jihar Zamfara ya bayyana ne a wajen wani babban gangamin shiyya inda jama’a kamar kasa suka taru a garinsu na Talatar Mafara da ke Jihar Zamfara.
“Hakika babu wata magana mai kama da haka, kuma ina jawo hankalinku saboda kuke yin zabe don haka ku Sani APC dai gida daya ce kuma ita za a yi daga sama har kasa.
“Kuma ina son a Sani cewa wannan taron na shiyya ne saboda haka za a tara taron jama’a da ake kira taron Jihar Zamfara baki daya a garin Gusau, inda kowa zai fahimci me ake kira da APC a Jihar Zamfara
Duk wanda ya halarci wannan taron ina mashi fatan alkairi da kuma taya murnar rungumar jam’iyyar APC da aka yi”.
“Akwai lokacin da za mu yi taron Jihar Zamfara baki daya da za mu hada kowace shiyya”.