Home / News / YA AKA YI DA KAYAN TALLAFIN JIHAR KATSINA NA KORONA?

YA AKA YI DA KAYAN TALLAFIN JIHAR KATSINA NA KORONA?

 

Mu’azu Hassan

@Katsina City News

Kwanakin baya Nijeriya ta shiga wani yanayi na wata zanga-zanga da ake kira ENDSARS daga baya ta rikide ta zama tarzoma, kisa, fasa shaguna da kone-kone.

Daya daga cikin abin da ya dauki hankalin duniya shi ne yadda aka rika fasa wasu sito-sito na ajiyar kayan abinci ana kwasa, lamarin da ya faru a Jihohin kasar nan da yawa ban da Jihar Katsina.

Kayan abincin an ce gwamnatin Tarayya ce ta ba da don raba wa jama’a saboda rage masu radadin kuncin rayuwa da aka shiga na halin da duniya ta samu kanta saboda cutar Koronabairus da ta bulla, kuma ta mamaye duniya.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da kayan tallafin

Irin wadannan kayan abincin da ke ajiye a sito-sito ne aka rika fasa wajen ajiyar ana kwasa a wasu Jihohin kasar nan ban da Jihar Katsina.

Gwamnatocin Jihohi sun yi ta bayanai daban-daban a kan wannan abinci da aka samu a kimshe har masu zanga-zangar suka wawashe su.

A Katsina wasu matasa sun rika yawo don su ga ko akwai irin wannan abincin da aka ajiye ba a raba wa jama’a ba don sun fasa su kwasa. Bayan yawo suka tabbatar babu suka hakura.

An yi ta rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta a kan yadda Jihar Katsina ta tsira daga wannan hali na fasa sito a Jihohi ana dibar abincin da ba a raba wa mutane ba.

A kan haka muka yi binciken ya aka yi, kuma wadanne irin kayan tallafi ne Jihar Katsina ta karba na Koronabairos? Kuma ya ta yi da su?

Mun gano cewa a duk Jihohin kasar nan, Katsina na daya daga cikin wadanda suka mayar da tallata duk wani motsin amsar taimako, ko yadda suka yi da gudummuwar da suka samu a kan COVID-19 a bayyane.

Kwamitin da aka dora wa nauyin kula da matsalar COVID-19 sun rika bayyana abin da suka tara ga manema labarai da kuma yadda suka sarrafa su.

Duk wanda ya shiga yanar gizo yana neman labarin tallafin COVID-19 labarin Jihar Katsina zai rika cin karo da shi a kan kudi da kayan da suka samu da kuma yadda suka yi da su.

Wannan ya nuna yadda kwamitin COVID-19 na Jihar Katsina bai bar tazara ba na bayyana wa duniya me jama’a, kamfanoni da gwamnatin Tarayya suka bayar tallafi a kan Covid-19.

Gwamnatin Jiha da kwamitin sun yi wani tsari na duk wani tallafin da aka kawo ake tsara ya za a rabar da shi ga wadanda ya dace ba tare da wani bata lokaci ba.

Kuma kowane kaya ko abin amfani za a yi masa kwamitin sama da mutum 10 wadanda za a tabbatar an dauko wakilai daga kowane bangare, a kuma rabar a gaban wakilan manema labarai na kafofin watsa labarai da na yanar gizo.

Wasu kaya da aka taba kawo wa gwamnan Katsina, Wanda kamfanin Dab I na yalium dake Kaduna ya bayar
shugabannin ’yan kasuwa suka roki a ba su su raba wa mutanensu. Gwamnan Jihar, Alhaji Aminu Bello Masari, ya amince. Shugabannin na ’yan kasuwa na Jiha suka je suka tsaro yadda za su rabar da su a Kananan Hukumomin da suka zaba, aka hada su da membobin COVID-19 na Jiha suka bi su suka tabbatar an rabar da kayan kamar yadda ya dace.

Jihar Katsina ta samu manyan taimakon kayan abinci na Koronabairos guda biyu. Na farko shi ne wanda manyan ’yan kasuwa, kamfanoni da Babban Bankin Nijeriya suka ba da. Ana masu lakabi da CA-COVID, wanda suka fara kawo rabin kayan kason Jihar Katsina a watan Maris, 2020. Kayan sune Shinkafa, Sukari, Gishiri, Taliya da Indomie, suka zo da tsarin suna son a raba wa magidanta dubu 67 da yadda za a rabar da su a Jihar Katsina.

Wadanda suka ba da kayan sun zo da tsarin yadda za a rabar da su a kan cewa Gwamnan Jiha ne zai jagoranci rabon kayan, sai mataimakinsa ya taimaka masa, sai wakilan CA-COVID, sai sauran membobin da za a nada.

Wadanda suka kawo kayan da ake kira da CA-COVID sun fara kawo rabi, suka ce za su kawo sauran. Don haka gwamnatin Katsina ta jira a ciko sauran kafin ta rabar, amma sai aka shiga kulle duk kasar da wasu Jihohi, ciki har da wasu yankuna na Katsina.

An jira sauran kaya ba a kawo ba. Don haka aka yi shawarar a rabar da wadanda ke hannu. Aka kafa kwamiti na Jiha, da na Kananan Hukumomi, da na Unguwanni da na Mazabu, ta yadda za a rabar da wadannan kayayyakin da ke hannu.

A ranar 12 ga Agusta, 2020 ne aka kaddamar da rabar da wadannan kayan a harabar babban sito na Jihar Katsina, wanda Maigirma Gwamnan Katsina da mataimakinsa da sauran jami’an gwamnati suka halarta. An kuma yayata rabon a duk kafofin sadarwa.

A wannan kason, kowace Karamar Hukuma ’yan kwamitin sun dauki nasu, kuma suka rabar. Kamar yadda aka tsara, kowace Rumfar Zabe za a zabo mutane shida da suka fi bukata ne a ba su. Babban Kwamitin na Jiha ya rika sanya ido da kasa kunne don ya tabbatar da an yi rabon kamar yadda aka tsara.

Ba kayan tallafin abinci Jihar Katsina ta samu ba a kan cutar Korona, ta samu an gina wani asibitin yaki da cututtuka masu yaduwa ne da ba kamar sa a duk Jihohin Arewa maso Yamma, aikin ginin da tuni aka fara shi. Hukumar maaikatan manfetur (NNPC) suke aikinshi.
kuma samu wasu motocin daukar marasa lafiya da kamfanin BUA suka ba da. Da gudummuwa daban daban daga mutane kuma duk an rabar dasu.

Amma duk da haka gwamnatin Tarayya karkashin Hukumar ba da Agajin Gaggawa (NEMA), su ma sun kawo nasu kayan bayan kullen hanya da aka yi ya yi sauki. Sun kawo Gero, Masara da Dawa. Gwamnatin Jiha na amsar kayan suka fara shirin yadda za su rabar da su, ta yadda kayan zai shiga duk lungunan Jihar baki daya.

Kwamitin Jiha da na Kananan Hukumomi da Rumfunan Zabe ya ci gaba da aikinsa na zakulo wadanda ya kamata su amfana a wurare daban-daban da wadanda suka amfana a shirin farko da kuma wadanda aka tsara za a ba in an kawo cikon tallafin CA-COVID.

Bayan an gama duk tantancewa a ranar 12/11/2020, aka fara rabar da kayan abinci da NEMA suka kawo, inda aka kaddamar a nan cikin birnin Katsina. Daga nan sauran Kananan Hukumomin suka dauka.

A kayan da Hukumar NEMA ta kawo, an tsara kowace rumfar zabe, gida takwas zai amfana da abincin da aka kawo, sune Gero, Masara da Dawa.

Yanzu akwai kayan da suka rage wadanda an tsara yadda za a rabar da su, an tantance wadanda za a ba. Sune mutane shida daga kowace Rumfar Zabe ta kayan CA-COVID, ta manyan ’yan kasuwa da kamfanoni da Babban Bankin Kasa (CBN).

Shi kuma abin da ya kawo tsaiko a rabar da su shi ne, sun fara kawo kayan abinci, amma da saura ba su kammala ba saura kiris, don bai wuce tirela daya da rabi ta garin Masara ba. Ko shi wannan an kammala tsarawa, an san wa za a bai wa in an kawo su. Rabo za a ci gaba da yi kamar yadda aka rabar da kashin farko.

Tsakanin kayan CA-COVID da kayan abincin da nema NEMA suka kawo, an tsara, kuma an rubuta adireshi da lambobin waya, ko katin zabe, ko shaidar katin dan kasa na mutanen da za su amfana da kayan tallafin.

Gidaje dubu 107 suka amfana da wannan tallafin. Gidajen kuma an tabbatar mabukata ne. A kowace Rumfar Zabe mutane 20 suka samu, ko za su samu, tunda akwai sauran kason da ba a kai ga rabawa ba, wanda ake jiran cikon sauran kayan. Shi kuwa kayan CA-COVID, gidaje dubu 67 ne. Kayan gwamnatin Tarayya na Hukumar NEMA kuma gidaje dubu 40.

Mun gano cewa yanzu haka akwai wani tallafin da ka samu daga gidauniyar TY Danjuma, wadanda suka ba da kayan abinci da suka hada da Masara, Shinkafa, Wake, man girki, kayan asibiti da kuma sinadarin wanke hannu, wanda suka ce a bai wa wasu da harin ’yan bindiga ya shafa a Jihar Katsina.

Wadannan kayan sune yanzu ake aiki a kan tantance yadda za a rabar da su ga wadanda abin ya shafa. Shi ma za a bi tsarin da aka bi na kwamiti ya gano wadanda suka dace don su amfana, kuma kayan su shiga duk inda abin ya shafa ba a tare da ajiye su a waje daya ba.

Mun tabbatar gwamnatin Katsina ta kashe kusan miliyan 100 na hidima ga wadannan kayan na tallafin da akan kawo mata. Hidimar da ta kama da magungunan kwari don kar su lalata su da dauko su da rabar da su zuwa kowace Karamar Hukuma zuwa Unguwanni zuwa Rumfunan Zabe. Duk wata hidima don aikin ya yi nasara gwamnatin Jiha ce ke daukar nauyi.

Kayan da aka samu a matsayin tallafi, ba kaya ba ne da za a ce za su iya karade kowane gida na mabukata a fadin Jihar Katsina. Sai dai a ce kaya ne da mai rabo ka samu.

Jihar Katsina na da gidajen mabukata sama da milliyan biyu , tana da yawan jama’a sama da miliyan bakwai. Manyan tallafin da aka samu an tsara gidaje dubu 107 ne za su amfana, kuma ba a wuri daya ba. Kowace Rumfar Zabe mutum 20 a duk fadin Jihar, don shirin ya shiga kowane lungu da sako. Amma abin da aka samu ba zai iya isar ko’ina ba, sai wanda Allah ya sanya da rabon sa.

Kuma aikin rabon an yi shi ne a karkashin kwamitin mutane masu mutunci daga Jiha zuwa Karamar Hukuma zuwa Rumfar zabe

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.