Home / Kasuwanci / Za A Samawa Maza, Mata Da Matasa Aiki A Najeriya – Aliyu Waziri

Za A Samawa Maza, Mata Da Matasa Aiki A Najeriya – Aliyu Waziri

Mustapha Imrana Abdullahi

Wani jagoran kokarin tabbatar da rayuwar jama’a ya kara inganta a tarayyar Nijeriya honarabul Dokta Aliyu Muhammad Waziri ya jaddada kudirin Gwamnatin tarayyar Najeriya na ganin an samawa Maza,Mata da matasa  ayyukan yi na bai daya ta hanyar koya masu kiwon Kaji.

Shugaban kungiyar Noman Zamani ta kasa Aliyu Muhammad Waziri da ake yi wa lakabi da dan marayan Zaki ya bayyana hakan a wurin taron kaddamar da koyawa mata, maza da matasa dabarun kiwon Kaji na zamani da aka yi a Kano, inda ya ce sun kammala shirin bayar da ayyukan yi ga mutane 64 aiki a kowace karamar hukuma.

Honarabul Aliyu Muhammad Waziri dan marayan zaki

Aliyu Waziri ya ci gaba da cewa Gwamnatin tarayya na da kyakkyawan tsarin samawa jama’a Maza, Mata da Matasa aikin yi domin dogaro da kansu a dukkan fannin rayuwa.

A wajen taron Daraktan kungiyar Noman Zamaninta kasa Alhaji Abdulhamid Yakubu cewa ya yi ana son tsarin tallafin ya zamo kaso Tamanin daga cikin dari ya zamanto wadanda za su ci gajiyarsa ya zama Mata ne saboda su ne ake mutuwa a kuma bar su da marayu, ko kuma Mazajen su gudu su bar iyalansu ba kuma hakan suke so ba duk hakan na faruwa ne sakamakon rashin abin duniya da suke fama da shi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa Abba Babanmaja kira ya yi a wajen su na kira ga shugaban wannan kungiyar da a samar da Injunan kyankyasar yayan Kaji a garin Kano.

Wanda idan an samu makyankyasar za a samu ci gaban da ya dace ta yadda al’umma za su amfana.

Hajiya Mai Jidda Abubakar daya daga cikin mahalarta taron bitar ta ce hakika ta amfana sosai musamman su mata da mazajensu ba za su bar su suna fita waje ba sai su rika yin abinsu daga cikin gida.

Sai dai a binciken da aka yi an gano cewa mafi akasarin kananan manoma da ake da su cikin al’umma mata ne da suka kasance kashi Ashirin cikin dari, saboda haka ana saran za a samu gagarumin ci gaba da wannan tsarin da Gwamnati ta samar domin koyawa Mata, Maza da matasa hanyar kiwon kaji domin ciyar da kasa gaba.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.