Home / Big News / Gwamnan Zamfara Ya Buƙaci A Ƙara Addu’o’in Zaman Lafiya Yayin Bikin Babbar Sallah

Gwamnan Zamfara Ya Buƙaci A Ƙara Addu’o’in Zaman Lafiya Yayin Bikin Babbar Sallah

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga al’ummar jihar da ma ɗaukacin Nijeriya da su ƙara dagewa wajen yin addu’o’in zaman lafiya da tsaro a yayin bikin Babbar Sallah na shekarar 2026.

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon taya murnar Babbar Sallah da ya aikewa al’ummar jihar a ranar Laraba, inda ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan babban biki na addinin Musulunci.

Babbar Sallah, wadda Musulmi ke gudanarwa duk shekara a ranar 10 ga watan Zul-Hijja, biki ne da ke nuna sadaukarwa da biyayya ga Allah, kamar yadda Annabi Ibrahim (A.S.) ya nuna cikakkiyar biyayya da miƙa wuya ga umarnin Ubangiji.

A cikin saƙonsa, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa nasarar jigilar maniyyata aikin Hajji kai tsaye daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa da ke Gusau, abin da ya bayyana a matsayin tarihi ga jihar.

“Ina taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar Babbar Sallah ta shekarar 2026,” in ji gwamnan.

Ya ce ibadar layya da ake gudanarwa a lokacin Eid el-Adha tana nuna biyayya irin ta Annabi Ibrahim (A.S.), sannan kuma tana daga cikin muhimman ibadun aikin Hajji da maniyyata ke aiwatarwa.

Gwamnan ya yi kira musamman ga al’ummar Zamfara da maniyyatan Hajji da su ci gaba da yin addu’o’i domin samun dawwamammen zaman lafiya da ci gaba a jihar da Nijeriya baki ɗaya.

Ya ce gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ’yan bindiga, lamarin da ya sa al’ummomin da suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-hare suka fara komawa yankunansu.

A cewarsa, a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar ta samu nasarar mayar da dubban mutane da suka rasa matsugunansu zuwa ƙauyensu na Fegin Kanawa da ke Ƙaramar Hukumar Gusau bayan sun shafe sama da shekara guda suna gudun hijira.

Gwamna Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da dawo da dukkan mutanen da rikice-rikice suka raba da muhallansu cikin aminci.

Ya bayyana cewa irin waɗannan nasarori ba za su samu ba sai da haɗin kai da addu’o’in jama’a, don haka ya buƙaci al’umma su ƙara himma wajen addu’a musamman a irin wannan lokaci mai albarka.

“Ina yi wa kowa fatan gudanar da bikin Babbar Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali,” in ji shi.

Daga bisani, gwamnan ya halarci sallar Eid tare da dubban jama’a a filin Idi na tsakiya da ke Gusau.

About andiya

Check Also

ADC; Ba A Yi Zabe A Shiyya Ta Daya Ba – Sama’ila Makarfi Da Ummu Lu’u Lu’un Matan Zazzau

….Zaben ADC Ya Bayar Baya Da Kura a shiyya ta daya Daga Imrana Abdullahi Ya’yan …

Leave a Reply

Your email address will not be published.