Daga Imrana Abdullahi
Bayan kammala gudanar da zaben fitar da yan takarar neman kujerun yan majalisar dattawa a yankuna Uku na Jihar Kaduna, shugabannin da suka jagoranci yin zaben a kowace shiyya karkashin jagorancin Malam Ladan Salihu sun tabbatar da zaben mutane Uku a matsayin yan takarar Sanatocin jihar karkashin jam’iyyar ADC.
Da suke yi wa yan jarida da sauran wadansu manyan mambobin jam’iyyar ADC jawabi a Otal din City Den da ke cikin garin Kaduna, baki dayan jagororin da suka jagoranci gudanar da zaben a kowace shiyyar mazabar dan majalisar dattawa sun tabbatar da mutane biyu da suka kasance suna kan kujerun Majalisar dattawa a yanzu a matsayin yan takara.
Wadanda aka tabbatar sun hada da Sanata Barista Ibrahim Khalid Soba a matsayin dan takara a shiyya ta daya da kuma Sanata Lawal Adamu Usman da ake yi wa lakabi da Mr LA a matsayin dan takara a shiyya ta biyu ko Kaduna ta tsakiya sai kuma Mista Godfrey Ali Gayya a matsayin dan takarar kujerar majalisar dattawa a shiyya ta Uku wato Kudancin Kaduna.
Bayan kammala bayyana sakamakon zaben Barista Ibrahim Khalid Soba ya yi jawabin godiya a matsayin yan takarar kujerun Majalisar dattawan inda ya yi godiya tare da yin addu’ar Allah ya kara tabbatar ma jam’iyyar ADC nasara a dukkan zabuka.
Sai kuma mutumin da zai yi wa ADC takarar Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Isa Ashiru Kusan, ya yi takaitaccen jawabi na godiya da kuma yin addu’ar samun nasara kamar mutum na farko.
Su dai Sanatocin da ke kan kujerun a jihar Kaduna sun ci zabe ne na hamayya kamar yadda wadanda suka gudanar da zaben suka bayyana.
THESHIELD Garkuwa