…Idan Zailani na da Jama’a ya koma wata jam’iyya
Daga Imrana Abdullahi
Sanata Shehu Sani mai takarar majalisar dattawa domin ya wakilci al’ummar yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa wanda ya kasance sanannen dan Gwagwarmayar kwato yancin jama’a ne da ya yi fice tun shekaru da dama da suka gabata a fadin Najeriya ya bayyana cewa yaushe ne Zailani Ya San Bola Tinubu hat yake yin wata kururuwa a Kaduna
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa tun bayan zaben shekarar 2015 ne ya kai Zailani wajen Tinubu, in ban da hakan yaushe ya san Tinubu.
“Ni Na kai Zailani wajen Shugaba Tinubu tun bayan zaben 2015, amma tun da na ji Zailani ya yaba mutuncin Gwamnan Jihar Kaduna hakika lallai Zailani ya rika fadin wadansu kalamai da ba haka suke ba domin ba daidai ba ne”, inji Shehu Sani.
Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin dimbin al’ummar Unguwar Tudun Nufawa da ke cikin garin Kaduna da suka kawo masa ziyara a gidansa da ke Unguwar Sarki Kaduna.
“Ta yaya mutumin da bai ci zabubbuka da dama ba da suka gabata inda ya na wata jam’iyya amma a karamar hukumar sa wata jam’iyyar daban da wani dan takara suka ci zabe sai ya rika yin wata kururuwa a cikin garin Kaduna
Dole ne da idan an yi zabe wasu su samu nasara wadansu kuma su fadi zaben hakan abin yake yin asalin zabe.
Kuma abin da Zailani bai sani ba dole ne su yi azumi kamar yadda wadansu suka yi a can baya sakamakon rashin cin zabe
THESHIELD Garkuwa