Home / Big News / Maza Da Matan Kaduna Ta Kudu Sun Kaiwa Sanata Shehu Sani Ziyara A Kaduna

Maza Da Matan Kaduna Ta Kudu Sun Kaiwa Sanata Shehu Sani Ziyara A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi
Dan takarar kujerar majalisar dattawa domin wakiltar mazabar yankin Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani, Ya yi kira ga daukacin mata da Maza da suka fito daga Unguwar Tudun Wada Kaduna da su kafa babbar kungiyar mata domin samun ci gaban da ya dace.
Sanata Shehu Sani ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da tawagar maza da Mata daga mazaba ta Shida daga Unguwar Tudun Wada Kaduna da suka kawo masa ziyara a gidansa, tawagar dai ta ƙunshi dukkan jama’a ne daga Kaduna ta Kudu
Sanata Shehu Sani kenan a cikin fararen kaya a ranar juma’a a gidansa yake yi wa tawagar Kaduna ta Kudu jawabi lokacin da suka ziyarce shi a kaduna
Sanata Sani ya yi kira ga matan da su shiga sauran Mazabu su jawo hankalin sauran mata da maza muhimmancin zaben Sanata Shehu Sani domin amfanin al’umma baki daya.
“Duk inda kuka ga ya dace ayi taimako domin a dole sai da hakan”.
Ku bi gidaje gidaje domin jawo hankali da fadakar da mata amfanin zaben Sanata Shehu Sani
“Ina gaya maku cewa kafin in zama Sanata sai da na fadi zabe sau biyu, haka shima Gwamna Uba Sani.
Wasu daga cikin tawagar Kaduna ta Kudu kenan
” Ku yi dukkan kokarin abin da Yakamata naku ya zama sanata a gobe
Wadanda muke takara da su lokacinsu ne bai yi ba ko kuma ya wuce don haka komai akwai lokacinsa
Wadansu kenan daga cikin tawagar da suka kawo wa Sanata Shehu Sani ziyara daga karamar hukumar Kaduna ta Kudu
Kuma ai wadansu sun samu nasarar zama yan majalisa a can baya har tsawon shekaru da yawa don haka ba wani abu idan Allah ya ba wadansu damar a yanzu.

About andiya

Check Also

Ba A Yi Zabe A Igabi Ba – Yan Takarar ADC

  Daga Imrana Abdullahi Daukacin yan takarar da ke neman jam’iyyar ADC ta tsayar da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.