Bayanan da muke samu a yau ranar 28 ga watan Mayu, 2026, na cewa an kaiwa Yan Kwamitin zaben Karamar hukumar Birnin Gwari mummunar hari inda aka ji masu raunuka jikinsu face face da jini.
Shi wannan wanann harin da aka kaiwa Yan Kwamitin zaben ana zargin cewa yan ta’addan siyasa ne suka kai shi, lamarin dai ya faru ne a a Layin Galadima inda ofishin Kamfe na Isa Ashiru yake a cikin garin Kaduna.
Daga cikin wadanda aka kai wa harin tare da ji masu rauni sun hada da
– Honarabul Abdullahi Muhammad Marafa Birnin Gwari
– Honarabul Yusha’u Ibrahim Abokin
– Honarabul Yakubu M Rabi’u
– Hinarabul Gambo Abdulqadir Gambo Kasace
Bayanan da muka samu sun ce tuni aka garzaya da wadanda lamarin ya faru da su na harin da ji masu rauni zuwa asibiti domin samun kulawa Likita cikin sauri domin ceton rayuwarsu.
Kamar dai yadda rahoton ya bayyana wadanda lamarin ya rutsa da su tuni sun samu kulawa a asibitin, sai dai akwai wani zargin cewa an yi wa rayuwarsu barazana a lokacin da aka kai masu harin.
Su dai wadannan yan ta’addan da suka kai harin ana zargin wani dan majalisa ne ya dauki nauyin su domin su aikata hakan.
Sai dai al’umma da dama sun yi Allah wadai da aikata wanann harin kamar yadda zaku iya ganin wadanda lamarin ya rutsa da su a cikin hoto.
An kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakin da ya dace, musamman na yin bincike a kan lamarin kuma Dukkan wadanda keda alhakin yin hakan an hukunta su bisa adalcin abin da suka aikata.
THESHIELD Garkuwa