Home / KUNGIYOYI / Arewa Media Writers Sun Karrama Gwamnan Jihar Zamfara

Arewa Media Writers Sun Karrama Gwamnan Jihar Zamfara

Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar marubuta da ke arewacin Najeriya ta Karrama Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Muhammadu Bello matawallen da lambar Yabo sakamakon aikin tukuru wajen ciyar da kasa gaba.
A wajen wani babban taron da kungiyar ta shirya a Kaduna da yayan ta suka samu halarta daga daukacin Jihohin arewacin Najeriya Goma sha Tara (19) baki daya sun bayyana cewa sakamakon irin yadda Gwamna Matawalle ke kokarin ganin an warware matsalolin da suke neman zama tarnaki ga kasar.
Gwamnan ya samu wakilcin Alhaji Ibrahim Magaji Dosara tsohon dan jarida kuma kwamishinan ma’aikatar yada labarai a Jihar Zamfara ya bayyana cikakken farin cikinsa da karramawar da kungiyar ta ba Gwamnan wanda ya nuna shaida ce ta gamsuwa da irin ayyukan alkairi da Gwamnan ke yi domin ciyar da Jihar Zamfara da  kasa gaba.
Dosara ya ce ” batun maganar lamarin yan bindiga a Jihar Zamfara ba lamarin ma’adanin zinare ba ne, wani lamari ne kawai na kisan da aka yi wa wani babban Bafilatani da su al’ummarsa suke ganin mutuncinsa, Kima da kuma daraja, hakan ya sa suka fara neman yin ramuwar gayya da ta kai ga halin da ake ciki a halin yanzu”.
Ya ci gaba da bayanin cewa Gwamnatin jihar Zamfara karkashin Dokta Muhammadu Bello Matawalle na iya bakin kokarinta domin ganin an samu kwanciyar hankali tare da karuwar arzikin jama’a.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.