Home / News / Babu Wata Mazabar Da APC Za Ta Fadi A Zamfara

Babu Wata Mazabar Da APC Za Ta Fadi A Zamfara

Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’Aziz Abubakar Yari ya bayar da tabbacin cewa saboda karbuwar jam’iyyar APC take da shi a Jihar Zamfara babu wani akwatin zabe ko mazabar da ake jin Shakkun cin zabe a duk fadin Jihar Zamfara.
Tsohon Gwamna Abdul’Aziz Yari Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja. Inda ya ce batun karbuwa da kuma lashe dukkannin zaben da za a yi ga jam’iyyar APC wani lamari ne mai sauki domin an rigaya an yi dukkan aikin da ya dace jam’iyyar ta samu karbuwa, kuma an cimma nasara don haka batun lashe zabe duk ba za a samu wata matsala ba.
“Mun yi taro tun a farko mun ce a ba mu kashi 80 cikin dari, aka ce a dai yi kasa kasa ana maganar kashi Hamsin Hamsin bangaren mu da na Gwamnan Zamfara na yanzu, amma wai shi ya na cewa a bashi kashi Saba’in mu kuma a ba mu kashi Ashirin amma hakan na mai yuwuwa ba ne ka gina komai a baka wani irin kaso”.
Koda yake an bar kyau tun ranar haihuwa duk da haka za a ci gaba da tattaunawa a tsakanin mu domin lalubo bakin zaren har a samu cimma nasarar da kowa ke bukata, har a zauna a sha shayi ana dariya idan kwalliya ta biya kudin sabulu”, inji Yari.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.