Home / News / Dokta Suleiman Ya Ba Maberaya Taimakon Kudi

Dokta Suleiman Ya Ba Maberaya Taimakon Kudi

…..Kuri’ar Maberaya Mun Baka, inji Musa Gwari
IMRANA ABDULLAHI DAGA SHINKAFI
Rashin adalcin karamar hukuma ne ace daga Maberaya zuwa Shinkafi ba hanya don haka nesa ta zo kusa za mu share maku hawaye al’ummar wannan gari na Maberaya.
An yi shugabanni da yawa me yasa ba su gyara hanyar Maberaya ba?
Kira ga matasa da dukkan yan Maberaya da su jajirce wajen ganin an zabi mutanen kirki
Ku taimakawa Gwamna domin ya fitar da hakkin da ke a wuyansa domin Gwamna na bada kudi, sai dai a tambayi shugabanni shin yaya abin yake
Lokaci ya yi a samu canji a matakin karamar hukuma, akwai kungiyar yan asalin Maberaya “da duk abin da ya same su a inda suke neman abincinsu da an ce su bar wurin da suke neman abincinsu da zarar sun gaya Mani zan shiga in fita da duk fadi tashin da zan yi domin kar su tashi a wuraren neman abincinsu haka kuwa lamarin yake, a halin yanzu suna can ba atayar da su ba wajen aikin Wankin mota da sauran sana’o’in da suke yi”.
“Ina yi wa Maberaya alkawalin cewa kudirina na farko shi ne zan zuba maku kwalta tun daga farkon hanyar nan zuwa garin Maberaya, don haka ku yi wa kanku kiyamullaili ku zabi nagari domin ku samu tsira da mutuncin kanku”, inji Suleiman Shu’aibu.
Matasa a taho ayi aikin nan na gayya domin magance matsalar Maberaya. Kuma game da wannan aikin na bayar da naira dubu dari (100,000) domin sayen abinci ayi aiki hanya.
Alhaji Aminu shugaban kungiyar ci gaban Maberaya, wannan rana ce ta tarihi da muka karbi bakuncin wannan shugaba na Gwawarmaya mai kokarin kwato yancin jama’a.
Muna sane cewa ” kai ka san yancin Talakawa don haka muka kafa kungiyar ci gaban Maberaya da ke fafutukar yin hulda da duk mi kishin garin mu kuma a shirye muke mu rabu da masu rashin kishin mu ba sauran romon baka.
A Farfado da duk hanyoyin magance matsalar Talakawa
Aminu, ya kuma bayyana batun fitowar da Dokta Suleiman ya yi na neman
Alhaji Musa Gwari, ya yi wa Dokta Suleiman alkawarin cewa ya ajiye komai sai ya ga Suleiman Shu’aibu ya dare kujerar shugaban karamar hukumar da ikon Allah.
Bunun Maberaya Alhaji Mande, mu muka hada kudi dubu dari biyu da Hamsin aka yi wa mutanen mu katin zabe domin mu kare mutuncin kanmu.
( A halin yanzu shal za mu yi a ranar zabe kai ne kawai muka Sani ba wata tantama, za mu gyara domin nemo yancin jama’ar Maberaya”.
Alhaji Gado Uban kasar Maberaya, godiya ya yi da ziyara da aka kawo garin Maberaya.
Muna jan hankalin mutanen Maberaya a ba Sarkin Shanu hadin kai da goyon baya, kasancewarsa jagoran yancin jama’a da ke fitowa a kafafen yada labarai ya yi magana a nemo yancin Talakawa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.