Related Articles
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce ba zai daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Damaturu a jihar Yobe ta yanke ranar Laraba kan zaben Sanatan Yobe ta Arewa da ke gabatowa ba inda ta dakatar shi daga shiga zabe.
Lawan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce ya amince da hukuncin da kotu ta yanke na hana shi takara da kuma shiga zaben.
Sanarwar mai taken: “Hukuncin Kotu kan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa” kamar haka:
“A jiya Laraba 28 ga watan Satumba, 2022, babbar kotun tarayya dake Damaturu ta yanke hukunci kan wanda ya cancanta ya tsaya takarar Sanatan Yobe ta Arewa a zaben 2023.
“Hukuncin da aka ce ya hana ni tsayawa takara don haka na aminta daa wannan hukunci na kotu .
“Bayan tuntubar juna da abokaina na siyasa da magoya bayana da masu da tsaki a mazaba ta cewar, na yanke shawarar ba zan daukaka kara kan hukuncin ba, na amince da hukuncin.”
“A halin da ake ciki, ina ganin ya dace in gode wa mai girma Sanata Ibrahim Gaidam bisa rawar da ya taka a siyasar jam’iyyar APC a jihar Yobe, ina kuma gode wa mai girma Gwamna Mai Mala Buni bisa goyon baya da ‘yan uwanta ka da ya nuna min.”
“Ga ‘yan mazabata, ina gode muku baki daya bisa goyon baya, biyayya da sadaukarwar da kuka yi na gina al’ummarmu da kuma gundumar Yobe ta Arewa da kuma jihar Yobe baki daya.”
“Ina so in tabbatar muku cewa zan ci gaba da yi muku hidima a cikin kaina da kuma kowane irin aiki a kowane lokaci.”
“Mun yi tafiya tare tsawon lokaci, kuma wannan tafiya za ta ci gaba da zama doguwar tafiya mai tsawo, dangantaka ce mai ban sha’awa kuma ba za ta iya katsewa ba I Allah ya so. Ina kuma tare da ku a kowane lokaci, Alhamdulillah.”