Daga Imrana Abdullahi
Dan takarar kujerar majalisar dattawa domin wakiltar mazabar yankin Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani, Ya yi kira ga daukacin mata da Maza da suka fito daga Unguwar Tudun Wada Kaduna da su kafa babbar kungiyar mata domin samun ci gaban da ya dace.
Sanata Shehu Sani ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da tawagar maza da Mata daga mazaba ta Shida daga Unguwar Tudun Wada Kaduna da suka kawo masa ziyara a gidansa, tawagar dai ta ƙunshi dukkan jama’a ne daga Kaduna ta Kudu

Sanata Sani ya yi kira ga matan da su shiga sauran Mazabu su jawo hankalin sauran mata da maza muhimmancin zaben Sanata Shehu Sani domin amfanin al’umma baki daya.
“Duk inda kuka ga ya dace ayi taimako domin a dole sai da hakan”.
Ku bi gidaje gidaje domin jawo hankali da fadakar da mata amfanin zaben Sanata Shehu Sani
“Ina gaya maku cewa kafin in zama Sanata sai da na fadi zabe sau biyu, haka shima Gwamna Uba Sani.

” Ku yi dukkan kokarin abin da Yakamata naku ya zama sanata a gobe
Wadanda muke takara da su lokacinsu ne bai yi ba ko kuma ya wuce don haka komai akwai lokacinsa

Kuma ai wadansu sun samu nasarar zama yan majalisa a can baya har tsawon shekaru da yawa don haka ba wani abu idan Allah ya ba wadansu damar a yanzu.
THESHIELD Garkuwa