Home / Big News / Muna Kira Ga Jama’a Da Ya’yan Jam’iyyar APC Su Hada Kansu Domin Samun Nasara – Shehu Sani

Muna Kira Ga Jama’a Da Ya’yan Jam’iyyar APC Su Hada Kansu Domin Samun Nasara – Shehu Sani

….Ni na dauki Kailani na kai shi wurin Tinubu bayan zaben 2015
Sanata Shehu Sani kuma ɗan takarar kujerar majalisar dattawa domin wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC ya yi kira ga daukacin ya’yan jam’iyyar da su tabbatar da samun cikakken hadin kai tare da yin aiki tare a koda yaushe domin samun nasarar da kowa ke bukata a zabe mai zuwa.
Sanata Shehu Sani ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin al’ummar Tudun Nufawa da suka kai masa ziyarar gaisuwar Sallah tare da tattaunawa domin sanin halin da yankin nasu ke ciki da nufin samun gyara mai ma’ana.
Alhaji Balarabe Abdullahi Sarkin Dutse Tudun Nufawa Kaduna, ya ce Tudun Nufawa Ana Barin mu baya domin ba a samu wata gwamnati da take kula wa da Tudun Nufawa ba, don haka muna son idan Allah ya bayar da nasara a yi wa Tudun Nufawa kokari su samu muhimman mukamai misali kamar na Kwamishina da dai sauransu ta yadda zamu bar wancan tsarin da bai san da yankin mu na Tudun Nufawa ba

Sarkin ya ce Tawagar shugabannin addinin Musulunci da Limamai da shugabannin siyasa daga Unguwar Tudun Nufawa da suka kawo wa Sanata Shehu Sani a ziyarar ban girma da karramawa.

Muna da kyakkyawar fahimta da Cikin Ekwa Coci amma akwai wani filin da suke da shi sama da shekaru ashirin da biyar amma sai ga shi an ba wasu sun gina bayin da za a rika yin bahaya da fitsari ana biyan kudi
.
Sarkin Dutse ya ci gaba da lissafin wadansu ayyukan da yankin nasa ke bukata kamar haka Gero road tsakanin Tudun Wada da Tudun Nufawa ruwa ya karya wannan Gada, muna kawo kukan mu ga Sanata da ya sanya baki ayi mana aikin domin jama’a su ci gaba da amfana.
Akwai wata babbar hanyar da ta ratsa daga kasuwa zuwa Tudun Nufawa har zuwa kusa da martabar Tudun Wada da Tudun Nufawa
Sanata Shehu Sani da yake mayar da jawabi cewa ya yi duk da an yi zaben fitar da Gwani a tsakanin yan takara kamar yadda aka sani wasu za su samu nasara wadansu kuma za su fadi.
Don haka muna kira ga wadanda ba su samu nasara ba da su rungumi ƙaddara a barwa Allah.
Akwai wadanda muka yi takara tare ta neman jam’iyyar APC ta tsayar da Dan takarar kujerar neman Sanata, amma akwai wadansu da suka shafe shekaru a majalisa suka shugabanci Mazabu shida har shekaru ashirin a ƙalla.
“Amma a mazabar Sanata Mazabu sama da Tamanin ne na jagoranta koda mutum bai san lissafi na ai zai san wanda ya fi yawa a tsakanin inda na jagoranta tsawon shekaru huɗu da wanda ya jagoranci Mazabu shida kawai”, inji Shehu Sani.
A cikin jam’iyyar APC kuma a cikin gwamnatin tarayya karkashin  shugabancin Ahmed Tinubu da akwai wadansu ministocin da suka ajiye aikin minista domin su tsaya takara misali kamar,Adelabu, ministan  Wutar lantarki, Akwai kuma ministan harkokin kasashen waje Tuggar ya ajiye aikinsa na minista don ya tsaya zabe akwai kuma ministan ayyuka da suka ajiye aiki don su tsaya takara, to ina ga wanda yake majalisar jihar Kaduna tsawon shekara a ƙalla ashirin, in yanzu mutum bai samu ba ai ba wani laifi bane domin an samu tsawon lokaci. Ana damawa”.
Akwai sanatoci 40 da suka tsaya takara duk a fadin Najeriya don haka muna fatan jama’a su rungumi ƙaddara.
Akwai yan majalisar wakilai da yawa sun shiga zabe sun rasa duk sun rungumi ƙaddara, don haka akwai samu akwai kuma rasawa idan an tsayar takara dole mutum ya san wannan.
Shi wancan dan takara da ya rasa zabe baya ga maciji da shugabannin jam’iyya, akwai batun rantsar da shugabannin jam’iyya a filin dandalin Murtala duk bai je wurin ba, ta yaya yan jam’iyya za su yi ka.
Akwai tarurrukan jam’iyya da yawa da aka yi wannan mutum bai zo ba.
An yi zabubbuka da yawa a Kaduna kuma duk inda yake yi wa goyon baya bai ci zabe ba.
Kamar yadda mutum ya saba cin zabe haka kuma wadansu ma suka saba ci suna faruwa
“Ni kabarin iyaye na duk suna nan a cikin garin Kaduna don haka ba wanda bai san Kwamared Shehu Sani ba a cikin garin Kaduna”.
“Ni da shi akwai alaka ta abokantaka,amma a siyasance ba mu tare”, inji Sanata  Shehu Sani.
” Muna da kyakkyawan zumunci da yan uwantaka tsakani na da Gwamna Uba Sani tun ma kafin ya zama Gwamna
” Ya dace duk wanda zai je majalisar dattawa ya nuna halin Dattako kafin ma mutum ya zama sanata a majalisar dattawa,kuma ya dace jama’a su sani ba a cin zabe da yan daban, kuma ba ta yadda mutum bai ga maciji da shugabannin jam’iyya Sannan mutum ya ci zabe.
“Yadda wadansu suka yi azumi dole ne kai ma sai ka yi, ta yaya baka shiri da dan majalisar wakilai,
Ni da bana fada da shi amma tun da na ji ya na kiran sunan Gwamna ya na yin wani tarihin da bai kamata ba da ba haka batun yake ba
Tun da Gwamna Uba Sani ya zama Gwamna ya na girmama kowa ba a taba wa yan kasuwa ko wani mutum ba Gwamna ya na girmama kowa a cikin jihar Kaduna, a yanzu Gwamna ya na kasar Makka kowa na San ya masa albarka
A nan Kaduna Ahmed Bola Tinubu, Uba Sani da Samata Shehu Sani duk za su ci zabe don haka wadansu dole ne su yi azumin da muka yi im lokaci ya yi za su Sha ruwa kamar yadda muka yi a can baya

About andiya

Check Also

Maza Da Matan Kaduna Ta Kudu Sun Kaiwa Sanata Shehu Sani Ziyara A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi Dan takarar kujerar majalisar dattawa domin wakiltar mazabar yankin Kaduna ta tsakiya …

Leave a Reply

Your email address will not be published.