Home / KUNGIYOYI / Matsalar Tsaro: Tambuwal, Masari, Matawalle sun nemi agajin tarayyar Turai

Matsalar Tsaro: Tambuwal, Masari, Matawalle sun nemi agajin tarayyar Turai

Matsalar Tsaro: Tambuwal, Masari, Matawalle sun nemi agajin tarayyar Turai

 

Mustapha Imrana Abdullahi

 

A kokarinsu na shawo kan matsalolin tsaro da ayyukan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso yamma, Gwamnonin jihohin da suka fi fama da wannan matsala, Sakkwato da Zamfara da kuma Katsina sun gana ranar Alhamis domin samun nagartattun hanyoyin da za a magance matsalar tsaron da ta shafi yankin. A kokarinsu na samun warware matsalar ne suka nemi agajin kungiyar tarayyar Turai da kuma kasashen Amurka da Kanada.

 

Taron wanda ya gudana a Sakatariyar kungiyar tarayyar Turai dake babban birnin tarayya Abuja. Taron wanda ya samu halartar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato da Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina da kuma Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara.

 

 

Babban jakadan kungiyar tarayyar Turai a Najeriya, Ketil Karlsen ya bayyana cewar  ta yi ma’ana domin samun bakin zaren warware matsalolin da suka kasance matsala da suka addabi wannan yanki, da kuma yadda matsalar tsaro ta Sahara a wannan yankin.

 

 

A cewar Karlesn, “dukkanmu muna da tsare tsare a kasa domin tunkarar wannan matsala a yankin Arewa maso yamma. Muna da ayyuka na jin kai da muka tsara kaiwa yankin, sannan kuma, mun shirya tattaunawa da ‘yan Siyasa a matakin tarayya da kuma kungiyoyin al’umma domin samun bakin zaren warware matsalar.

 

 

“A shirye muke mu bayar da dukkan gudunmawar da zamu iya, wajen ganin an samu dawwamammen zaman lafiya a wannan yanki, tare da ganin cewar mun taimaka wajen dinke duk wata baraka dake damun wannan yanki musamman ta bangaren Ilimi da kiwon lafiya da sauran matsalolin da zamu iya taimakawa. ” A cewarsa.

 

Ya kara da cewar, babbar hanyar samun cikakken zaman lafiya mai dorewa ya ta’allaka ne da irin gudunmawar da Gwamnatin tarayya ta bayar a wadannan yankuna da wannan rikici ya shafa.

 

 

A koda yaushe, a shirye tarayyar Turai take domin ganin ta bayar da gudunmawar ta wajeb kyautata rayuwar al’umma musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, kuma tarayyar Turai zata samar da damarmaki domin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa.

 

 

A yayin da yake maida martani, Gwamnan jihar Sakkwato Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal CFR ya bayyana cewar, wannan ganawa ta musamman ce da aka yi da abokai na gari domin samun bayanai da zasu iya kawo karshen wannan matsala da ake fama da ita. Ya kara da cewar, a irin wannan yanayi dabake ciki dole ne mu taimaka da Gwamnatin tarayya da dukkanin wasu bayanai da zasu kai ga kawo karshen matsalolin nan”.

 

 

Ya ci gaba da cewa, Gwamnonin wadannan yanki, a shirye suke da dukkan wani tallafi da za su samu na kawo karshen matsalar tsaro tare da taimakon Gwamnatin tarayya.

 

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, a nasa bangaren, ya bayyana cewar “mun nemi taimako ne daga bangaren tarayyar Turai da fatan hakan zai haifar da d’a mai ido nan ba da jimawa ba”.

 

 

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara kuwa cewa yayi, yana da kwarin guiwa cewa kasashen waje a shirye suke wajen suga sun taimaki Najeriya musamman ya kin Arewa maso yamma dan ganin an dakile matsalar tsaro.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.