Home / Labarai / Hajiya Aminatou Abdoulkarim Muhammad Alakiri Ce

Hajiya Aminatou Abdoulkarim Muhammad Alakiri Ce

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna.

Wadansu masu kishin al’ummar kasar Janhuriyar Nijar mazauna Najeriya sun bayyana Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad da cewa alkairi ce ga kasashen Najeriya da Nijar.

Wadansu mata ne da suka Dade a tarayyar Najeriya tun suna yan kananan yara suna tare da iyayensu har a yanzu sun kai zama iyaye da kakannin wadansu suka bayyana hakan domin su shaidawa irin kokarin da Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad da ke Abuja ta yi wajen hasa kan daukacin al’ummar Nijar da suke a Najeriya.

Wata mata mai suna A’ishatu ta ce tun ta na yar shekaru 12 ta na a gaban iyayen ta take a Najeriya ba a taba samun wani shugaban da yazo har ya ce shi ne wane ko su ne wane da wane ba sai Hajiya Aminatou Abdiulkarim kawai ita kadai ta ke wahala da jama’ar Nijar da kai maku ziyara ta lalubo ku duk a inda kuke ta fadakar tare da wayewa al’ummar Nijar mazaunan Najeriya da kawunansu har sun san yancin su a matsayinsu na yan Nijar.

” Akwai lokacin da wani mutum bashi da lafiya har Allah ya karbi ransa a wani asibiti kuma ga kudin magani sun taru sama da naira miliyan daya an kuma ce ba za a bayar da Gawarsa ba sai an biya kudin, my dai ba mu san kowa ba sai ga Hajiya Aminatou ta zo nan da nan ta tashi ta samu tsohon Ambasada aka san yadda aka warware duk lamarin nan baki daya. Kuma ni a iya zamana a Najeriya ban ma san akwai ofishin jakadancin Nijar a Najeriya ba sai dalilin Hajiya Aminatou Abdoulkarim Muhammad da ke zaune a Abuja, don haka me wani mutum zai gaya mana wai ace shi shugaba ne”, inji ta.

“Kai muna nan a Najeriya wallahi ba ma son ma a ce mu yan Nijar ne saboda halin da mutum zai shiga a bangarorin gudanar da rayuwa da dama, amma zuwan Hajina Aminatou an samu nasarori kwarai a tsakanin al’ummar Nijar mazaunan Najeriya”.

A’ishatu ta ci gaba da cewa ta na a Najeriya tun ta na yar shekaru 12 a gaban iyayen ta amma ba wani da ke zuwa ya na Hidimtawa yan Nijar balantana ma su san wai suna da jigo”.

Ita ma da take tofa albarkacin bakin ta Hajiya Hajara cewa ta yi haduwa da Dokta Amonatou da ke zaune a garin Abuja alkairi ne domin mutum ne ya hadu da dan uwansa wanda bai Sani ba amma dalilin wannan baiwar Allah an hadu kuma an san Juna, an yi zumunci an kuma fadakar da jama’a don haka sai dai kawai ace wa Hajiya Aminatou, Allah ya biya ta da Aljannah kawai domin ta yi aiki

“Kuma tun a can baya muna da shugabannin yan jam’iyyar tarayya amma ba mu san dadin komai ba sai dalilin zuwan Hajiya Aminatou Abdoulkarim Muhammad don haka alkairi ne kwarai Dokta Aminatou ta kawo mana saboda zaka ga mutum ya hadu da dan uwansa da suke a gari daya amma bai san shi ba sai dalilin aikin da Hajiya Aminatou ta yi har kowa ya san kowa tsakanin Juna, kunga wannan aikin ba na wasa ba ne domin gagarumi ne”.

Da akwai wata matar ma a kwanan baya da ta ce ta na zaune a layin Kerawa a Unguwar Tudun Wada Kaduna ta na zaune a wurin tsawon sama da shekaru 45, amma ba wanda ya ta ba zuwa ya nuna mata ya san abin da take ciki ko da sunan wani shugabanci sai Hajiya Aminatou Abdoulkarim Muhammad, domin ita ce kawai ta san abin da jama’a suke ciki saboda irin damuwar da ta yi da rayuwar yan Nijar, wanda a koda yaushe kokarin ta shi ne rayuwar jama’a ta inganta.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.