Home / Uncategorized / An Yi Kira Ga Bola Ahmad Tinubu Kan Lamarin Tsaro

An Yi Kira Ga Bola Ahmad Tinubu Kan Lamarin Tsaro

Daga Imrana Abdullahi

An Yi Kira ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya kara matsa kaimi wajen tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a a tarayyar Najriya.

Alhaji Aliyu Muhammad Waziri ne y yi wannan kiran a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna.
Aliyu Muhammad Waziri, Santurakin Tudun wada Kaduna ya ce hakika akwai bukatar Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmad Tinubu ta kara himmatiwa domin kara inganta al’amuran tsaro a fadin kasar.
Sai dai Aliyu Muhammad Waziri wanda ke rike da sarautun gargajiya da yawa ya bayyana wadanda ke yin mulki a kasara jamhuriyar Nijar a matsayin mutanen da suka yi fashin kwatar mulkin wanda ya ce hakika ya sabawa tsarin dimokuradiyya baki daya.
“Ko a can baya babban dalilin da yasa na yi ta sukar abin da ya faru a kasar Nijar din saboda ya saba wa tsari da tanaje – tanajen dimokuradiyya ne don haka nake ta yin kalubale a kan lamarin”.
An kuma yi gagrumin bikin murnar sunan yayan da aka haifawa masa guda biyu da ya sanya wa suna Nana Khadija da Nana Bilkisu da dimbin jama’a suka halarta daga ko’ina a duk fadin Najeriya.

Makada da mawaka da dama da aka gayuace su duk sun baje kolinsu a wajen gagarumin taron sunan, daga cikin mawakan da aka gayyata sun hada da Alhaji Musa Dan bade, Alhaji Shehu Ajilo da sauransu da dama

About andiya

Check Also

Babbar Sallah: Gwamna Lawal Ya Buƙaci Musulmin Zamfara Su Tuna Da Muhimmancin Sadaukarwa Da Halin Ƙwarai

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya taya al’ummar Musulmin Zamfara da Nijeriya murnar zagayowar …

Leave a Reply

Your email address will not be published.