Hadin Kai Da Jajircewa Ne Zai Tabbatar Da Dimokuradiyya – Shetland Yerim
Daga Imrana Abdullahi
A kokarin tabbatar da dimokuradiyya da samun ci gaban kasa tare da al’ummarta yasa Shugaban ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (AYCF), kwamared Alhaji Yerima Shettima ya bayar da tabbacin cewa sai da hadin kai da jajircewa ne mulkin damakuradiyya zai tabbata a tarayyar Nijeriya.
Kwamared Shetima ya bayyana haka ne a wani taron gangamin da aka shirya domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai wanda ya gudana a Jihar Kaduna.
Yerima Shettima, wanda yana daga cikin masu neman takarar kujerar Dan majalisar dattawa daga tsakiyar jihar Kaduna, ya kara da cewa lokaci Yayi da al’ummar kasar nan zasu rungumi zaman lafiya da hadin kai domin ganin kasar ta ci gaba ta bangarori da dama.
” ina mika gaisuwar fatan alheri ga duk ‘yan Nijeriya yayin da muke bikin cika shekaru 65 na ‘yancin kai. Ƙasarmu mai daraja ta sha wahala ta hanyar sadaukarwa, juriya, da ƙudurin zuciyar jama’arta. Yayin da muke murna, mu rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ɗa’a a matsayin ƙa’idojin rayuwarmu ta ƙasa”
” Sai da haɗin kai da jajircewa tare ne za mu iya tabbatar da dimokuraɗiyya da kuma gina kyakkyawar makoma ga al’ummomi masu zuwa”
” ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummomi, da fadin ƙasar. cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu, da hakan muna murnar Barka da ranar ‘Yancin Kan Najeriya.
Shettima ya jinjinawa kokarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na samar da abubuwan ci gaban kasa da ya ce idan aka kara hakuri abubuwa za su yi kyau a duk fadin kasar baki daya.
Taron wanda kungiyar yakin neman zabensa mai suna (Capacity Movement) ta shirya ya samu halartar matasa daga sassa daban-daban na jihar Kaduna da kungiyar ‘yan Keke-napep da ‘yan acaba da kuma masu amfani da Manya manyan mashina ( bike) tare da manyan motoci da kanana duk sun hakarci gangamin da aka yi a Kaduna.
THESHIELD Garkuwa