Home / Big News / Hadarin Motar Shanu; An Bukaci Gwannati Ta Samar Da Mafita Kan Karancin Motoci

Hadarin Motar Shanu; An Bukaci Gwannati Ta Samar Da Mafita Kan Karancin Motoci

Alhaji Abubakar Inuwa shugaban kungiyar Falaken Shanu a tarayyar Najeriya kuma Alkalin kungiyar kuma Dan kwamitin amintattu a jihar Adamawa ya bukaci Gwamnatocin tarayya da Jihohi da su hanzarta samawa Jama’a mafita a Kan batun karancin motocin daukar fasinja da na Fataucin Shanu domin a magance matsalar da ke Fuskantar bangarorin biyu.

Alhaji Abubakar Inuwa ya yi wannan Kiran ne a lokacin da Yake ganawa da wakilin mu ta wayar Salula a game da irin matsalar da ke tartare da batun Fataucin Shanu da kuma motocin daukar al’umma da Ake yin sufuri da su.

” Hakika muna samun bayan matsalar da Ake samu wajen daukar Shanu inda Ake samun Jama’a da dama na Hawan Saman motocin daukar Shanu zuwa Legas KO kuma yankin Kudancin Najeriya daga yankin Arewacin kasar,Wanda Sakamakon hakan Ake samun hadarin da ke sanadiyyar rasa rayuka da kuma dukiyar, don haka muke yin addu’ar Allah ya gafarta WA wadanda suka rasa rayukansu ya kuma ci gaba da kiyaye mu Baki daya”.

“A matsayin mu na shugabannin kungiyar Falaken Shanu a tarayyar Najeriya muna nan muna tattaunawa muna kuma duba yadda Lamarin Yake da yadda za a shawo kansa Amma abin da muka Fara ganowa Shi ne akwai matsalar karancin ababen Hawa da Jama’a ke Fuskanta, saboda idan Ka ga mutum a Saman tirela zaka tarar ya biya a kalla naira dubu Goma ne a Kai Shi har Legas, a madadin ya biya naira dubu Saba’in a karamar mota KO dai Mai daukar mutane kawai BA Kaya KO Shanu BA, kuma wani idan ma ya na da naira dubu Saba’in BA zai ta fi Legas KO wani wuri Neman Kudi BA, don haka sai gwannati ta duba wannan batu da nufin yin maganinsa kowa ya samu sauki”.

Abubakar Inuwa ya ci gaba da cewa,”sun gano cewa batun sana’ar Yan Gwangwani na taimakawa wajen haifar da karancin motocin da kuma Tsadar su domin idan a yanzu kana da tsohuwar mota idan na sayar da ita naira miliyan biyu idan Ka je da naira miliyan Uku BA zaka samo wata Ka mayar da ita BA, don haka Jama’a BA su da wani Zabi wajen Hawan motocin a yanzu kamar dai irin yadda za a GA ni a kasar Indiya mutane na makale jirgin kasa”, inji Inuwa.

Inuwa ya Kara da cewa a bangaren masu motocin kuma akwai rashin sayo motocin Wanda hakan ma ya Kara WA motocin tsada saboda karancinsu.

“Don haka ne muke yin Kira ga Gwannati da Babbar murya da don Allah a duba wannan yanayin da muke Ciki daga mu masu Sana’a irin ta mu da kuma masu sufurin Jama’a da su jama’ar kansu.

About andiya

Check Also

Dangote headlines 2026 Gateway Trade Fair as Gov Abiodun hails Group for boosting Ogun’s Industrial Competitiveness

Ogun State Government has lauded the roles being played by the Pan-Africa conglomerate, Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.