Home / Big News / Manoma Na Cikin Akuba A Najeriya – Kungiyar Manoma

Manoma Na Cikin Akuba A Najeriya – Kungiyar Manoma

 

Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon irin tsananin akubar da harkar Noma da masu yin Noman suka Shiga ciki a Arewacin Najeriya ya sa shahararriyar Kungiyar manoma zalla na gaskiya daga Arewa Maso Yammacin Najeriya, Mai suna ( North West Agricultural Commodities Association) suka fito fili inda suka kokawa Gwannatin tarayyar Najeriya da ta mayar da hankalin ta Wajen inganta harkar Noma ta yadda za a samu ingantar tattalin arzikin Jama’a da na kasar Baki daya.
Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar mai suna Alhaji Shu’aibu Idris Mikati, ya bayyana hakan a wajen wani taron Manema labarai da kungiyar ta Kira da aka yi a Otal din Gombe Jowell a cikin garin Kaduna.
Alhaji Mikati tare da dimbin yayan kungiyar sun fayyace karara a fili cewa idan fa aka nakasa harkar Noma a Najeriya hakika za a Shiga cikin mummunar matsalar rashin aikin yi da kuma lalacewar tattalin arzikin kasa Baki daya.
” Ta yaya Manoma za su sayi Takin zamani a Kan makudan kudin da suka Kai Sama da naira dubu dari, wani buhuna Takin kuma a Sama da naira dubu Hamsin sannan GA Tsadar Sauran Kayan Noma tun daga Feshin ciyawa zuwa Feshin kwari da Feshin Takin zamani sannan a rika sayar da buhun Kayan Noma a Kan kudin da BA su taka Kara suka karya BA idan an yi la’akari da irin makudan kudin da Manoma ke kashewa kafin su Samar da kayan abincin da Jama’a da kuma Kamfanoni ke bukata.
Mikati ya kuma CE idan fa BA a yi Noma kamar yadda ya dace BA za a iya samun matsalar mummunan karancin abinci Wanda hakan Ka iya haifar da abin da BA a fatar na Yunwa da Shiga matsalar karyewar tattalin arzikin kasa
“Indai shugaban Tinubu da gaske Yake yi cewa tattalin arzikin kasa ya Kai Tiriliyan daya na Dolar Amurka to fa sai an taimaki Noma.
Muna Kira GA Gwamnonin Arewacin Najeriya su yi koyi da Gwamnonin yankin Kudu Maso Yamma inda suke tattaunawa su taimaki yankinsu.
Manoman Najeriya na cikin wani halin kakanika yi tun daga halin rashin tsaro da kuma hauhawar Farashin Kayan yin Noman da Sauran wadansu matsalolin da dama.
Amma duk da haka sai GA Shi Farashin Kayan Noma duk ya yi kasa warwas.har ta Kai GA sai manomi ya sayar da Masara akalla buhu Uku sannan ya sayi buhuna Takin da zai yi amfani da Shi.
“Akwai fa wata matsala in fa BA a yi WA Manoma adalci ba za a iya wayar gari Yunwa da rashin abinci su afkawa Najeriya abin da BA a fatar ya faru, wane kamfanin Sabulu KO Fulawa NE ke sayar da kayansa a Kan faruwar Farashin idan akwai a fito a Fadi.
Misalin, ” Gwannatin Buhari ta bayar da bashing Noma GA Manoman Shinkafa da Masara da Sauran su Amma a yanzu BA komai sai ma Noman Nema Yake ya Zama abin da BA za a iya yinsa BA.
“Akwai wani Kudiri a gabanajalisa na Trust receid a Gabatar da ita domin dokar ta samawa Manoma sauki.
Gwannati,Bankuna da Sauran masu Hannu da shuni lallai su zo su taimaka wa Manoma.
“Mu idan an zo zamu bayar da Shawara Kyauta ta yadda za a samu ci gaba
Aje Indiya KO Indonesia a samo taraktocin Noma masu saukin sarrafa wa, kuma KO a kasar Amurka na bayar da tallafin Noma har ma akwai lokacin da Amurka ke diban alkama ta Zuba a Teku domin Kifi ya samu abinci Kada Manoma su su yi asara.
“Ta yaya Gwannati za ta Bude kofar shigo da kayan abincin da Ake nomawa Amma BA wani Shirin taimakawa manoma

About andiya

Check Also

Dangote headlines 2026 Gateway Trade Fair as Gov Abiodun hails Group for boosting Ogun’s Industrial Competitiveness

Ogun State Government has lauded the roles being played by the Pan-Africa conglomerate, Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.