Ministan Tsaro na Ƙasa, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa sayo motoci masu sulke, jiragen sa-ido marasa matuƙa (drones) da sauran kayan aiki domin ƙarfafa wa rundunonin tsaro a jihar.
A wani biki da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Gusau ranar Laraba, Gwamna Lawal ya miƙa motoci 25 na zamani masu sulke (Armoured Personnel Carriers) ga jami’an tsaro, domin ƙara musu kariya yayin da suke gudanar da aiki a yankunan da ke da haɗarin tsaro a faɗin jihar.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa baya ga motocin sulken, gwamnatin Zamfara ta sayo jirgin sa ido mai ƙarfin shawagi na tsawon mita 80, wanda zai iya rufe nisan kilomita 50 tare da yin aiki na tsawon sa’o’i takwas ba tare da tsayawa ba.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da kayayyakin, Gwamna Lawal ya ce halartar Ministan Tsaro ta ƙara nuna haɗin kai da fahimtar juna tsakanin Gwamnatin Tarayya da ta Zamfara wajen tabbatar da tsaro da doka a jihar.
Ya bayyana cewa tsawon shekaru, Zamfara ta fuskanci matsalar tsaro da ta kawo cikas ga rayuwar al’umma, noma, kasuwanci da zirga-zirga, lamarin da ya shafi tattalin arzikin jama’a.
Ya ce a karƙashin shirin “Rescue Mission”, gwamnatinsa ta koma daga martani na wucin-gadi zuwa tsarin gyara mai ɗorewa, inda aka kafa Asusun Tsaro na Jihar Zamfara domin samar da ingantaccen tallafin kayan aiki ga hukumomin tsaro. Haka kuma, an samar da rundunar tsaron al’umma, wato ‘Community Protection Guards’ bisa tanadin doka domin inganta tattara bayanan sirri da sama da tsaro.
Gwamnan ya ƙara da cewa, gwamnati ta raba motocin Hilux sabbi 150 ga jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda, DSS da NSCDC, tare da sayo motocin Toyota Buffalo guda 20 – 10 masu sulke da 10 marasa sulke – da kuma babura sama da 600 domin saurin kai ɗauki a wuraren da ababen hawa ba sa iya shiga cikin sauƙi.
Ya jaddada cewa haɗa sa ido ta sama da ta ƙasa zai ƙara faɗaɗa hangen nesa na jami’an tsaro, inganta fahimtar yanayin wuri da kuma ƙarfafa daidaito tsakanin cibiyoyin umarni da jami’an da ke fagen daga.
A nasa bangaren, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce matakin da gwamnatin Zamfara ta ɗauka na sayo motocin sulke da sauran kayan aiki ya nuna ƙwazon jagoranci da jajircewar gwamnan wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Ya bayyana cewa, duk wani shugaba da ke zuba jari mai tsoka wajen tsaron jama’arsa yana aikewa da saƙo mai ƙarfi ga masu aikata laifi.
Ya ƙqra da cewa, kare rayuka da dukiyoyi ya wuce siyasa, yana mai nuna farin cikinsa da yadda gwamnatin Zamfara ta biya dukkan kuɗaɗen kayan aikin gaba ɗaya, lamarin da ke ƙara tabbatar da ƙudurin gwamnati na yaƙi da rashin tsaro.
THESHIELD Garkuwa