…zan ba Gwamna kujerarsa in ya kammala
Daga Imrana Abdullahi
Fatan da nake yi kuma bukata ta abin da muke fata na alkairi shi ne Gwamnan mu Uba Sani Allah yasa ya ci gaba da yin nasarar a shugabancin da yake yi ya zamanto tun da ake yin Gwamna a Jihar Kaduna ya zamanto ba a samu wanda ya yi wa jama’a adalci kamar Uba Sani ba.
Dan takarar neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar kujerar majalisar dattawa a yankin shiyyar Kaduna ta biyu da ake kira, ( zone 2) ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa al’umma jawabi a lokacin da ya kai ziyara ofishin jam’iyyar na jihar Kaduna.

“Abin da nake son in gayawa wannan babban taron jama’ar da suka taru a nan shi ne fatana samun nasarar Uba Sani, don haka na yi alkawarin idan Allah ya kai mu ga nasara Burina shi ne nasara da ci gaban Kaduna din haka ina son idan na samu karo na farko shekaru Hudu da Allah ya ba ni, zan rike ma Gwamna amana in Allah ya sa ya kammala shekaru Takwas dinsa na Gwamnan Kaduna idan ya zo ya na bukatar zai zama Sanata zan ba shi kujerarsa, idan kuma Allah ya kawo wani abu mafi hakan ina yi masa fatan alkairi zamu ba shi goyon baya amma Ni mazaba ta ce guda daya kawai domin Ni ba Ni da wani dogon buri saboda ita kanta siyasar har sai na mutu a cikinta ba ne, A’a na kawo ta ne domin ya kasance a cikin mutane da akwai wadanda Allah ya yi su masu imani da tausayi ga Al’umma da za su kawo ci gaba shi ne maganar, ina yi wa kowa godiya.
Tawagar Kwamared Shettima Usman Yerima dai ta samu kyakkyawar tarba daga shugabannin jam’iyyar na Jihar Kaduna baki daya inda suka yi masa lale marhabin shi da tawagarsa baki daya.

Kuma a nan gaba za mu ci gaba da kawo maku irin yadda jawabai suka gudana a wajen wannan taron ziyara mai cike da dimbin tarihi a ofishin jam’iyyar APC na Jihar Kaduna da Kwamared Shettima Yerima ya kai domin jaddada takararsa ta sanata.
THESHIELD Garkuwa